Wani Bazazzagen tela ne surikinsa ya ba shi dinki, sai ya sanya masa ranar da zai zo ya karba. Da ranar ta zagayo, Sirikin ya zo karbar dinki, sai ya kasance tela bai gama dinki ba. Sai telanka ya ce da surukin nasa: “Baba ka yi hakuri, ban dinka ba amma ka dawo gobe ka karba.”
Washegari tela yana zaune a kofar shagonsa yana hira da abokansa sai ya hango surikinsa yana zuwa, ai kuwa sai ya ruga ya shiga shagon, ya ce da abokan aikinsa da su yi sauri su rufe shi da kyallayen yadi, ya kuma ce idan surikin nasa ya zo, su fada masa cewa ya yi tafiya. Ashe wajen rufe shi sun mance ba su rufe kafafunsa ba.
Da surikin ya karaso shagon, sai telolin suka isar da sako kamar yadda tela ya bari.
Surikin ya yi kamar ya yarda, ashe ya ga kafafun telan a waje, sai ya ce wa telolin: “Ku shaida masa cewa nan gaba idan zai yi tafiya, ya daina tafiya yana barin kafafuwansa.”
0 comments: