A lokuta da dama mu kan samu kan mu a wani hali na rashin ci gaba. Duk kokarin muga al’amura sun chanja su kasa cimma ruwa.
Idan haka ta faru ne sai kaga wasun mu sun fara nuna yatsa. Ai wancan ne ya janyo min, ko kuma duk laifin wane ne. Wasu ma har su kai da cewa asiri aka yi musu.
Sai kuma masu dangane komai da kaddara. Bawan Allah baka futa nema, ba aljihun ka ba ko sisi, ka ce wai kaddare ce. Baiwar Allah ba ki je asibiti ba ciwo ya ci tura ki ce wai kaddara ce?
Da a ce zamu nutsu, zamu fuskanci cewa halayen mu da irin tunanin mu da gazawar mu a sau da yawa su ne silan rashin cimuwar gaba.
Ga wasu daga cikin irin halayen da nake nufi
Rashin godiyar Allah Da yawan korafe korafe
A ko da yaushe kai dai bata maka ake yi. Kullum rayuwa bata maka dai dai. Ka yi korafin wannan ka yi korafin wancan. Yan gida basu tsira ba abokan aiki ko kasuwancin ka basu tsira ba.
Duk dadin yanayin da kake ciki sai ka sami abin da zaka yi korafi a kai.
Abunda baka sani ba shine, a duk lokacin da hankalin ka ya karkata wajen ganin abin da yake ba dai dai ba, toh shi kadai zaka ci gaba da gani. Hakan kuma shi zai ci gaba da faruwa a rayuwar ka.
Duk wanda ka gani yana numfashi, to fa yana da matsalolin rayuwa. Bambancin kawai shine, wasu sun fi ta’allaka zuciyar su ga alkhairan da ke rayuwarsu, kuma a kullum suna cikin godewa Allah da baiwar da ya yi musu.
Idan ka yi karatun ta nutsu, zaka fuskanci cewa kaima kana da su babu iyaka. Allah ya kan saka wa mai godiya da karawar rahamomin da zai kara yin godiya a kan su.
Jiran sai rana ta fadi
Kai dai ba ka san wahala. Rayuwarka tana bukatar ka dau wasu kwararan matakai da zasu ci da kai gaba amma kullum jira kake sai lokacin da ya fi sauki. Sai anyi magana kace mai hakuri Yana tare da Allah. Toh wai a ina jira da hakuri su ka zama daya?
Hakuri shine ka zage damtse kayi ta yin iya kokarin ka duk da baka san yanda sakamakon zai kasance ba. Hakuri shine kayi ka fadi ka kara gwadawa. Hakuri shine ka jure kayi duk rashi dadin sa.
Amma jira fa? Ka kasa katabus, gobe ta zama jibi, jibi ya zama sati mai zuwa, sati mai zuwa ya zama watan gobe. Haka dai haka dai rayuwar tai ta tafiya.
Ka sani fa babu wani ci gaba da yake wanzuwa a cikin sauki. Dole sai ka juri yin abubuwan da baka so.
Mu daina yaudarar kanmu. Hakuri yana haifar da ci gaba, jira kuwa lalata damar samuwarta yake.
Rashin yarda da baiwar da Allah yayi maka
Ubangiji ya haliccemu ne cikakku kuma ya bamu duk wata baiwar da zamuyi amfani da ita mu ci gaba a rayuwar mu.
Sai dai wani lokacin, irin horon da muka samu tun muna kanana, da irin alummar da muka tashi a cikin ta, da halin rayuwa da muka tsinci kanmu a ciki, har ma da irin tunanin mu, su kan taruwa su dakushe wannan baiwa da Allah yayi mana.
Amma fa wannan ba hujja bace. Duk wanda ka gani ya cimma gagarumar nasara to shima akwai lokacin da ya tsinci kansa a irin wannan halin. Bambancin kawai shine yayi kokari wajen sauya tunanin sa na nakasu, ya fara amfani da baiwa da kuma damar da Allah yayi masa.
Ka daina gaggawar fada ma kanka bazaka iya ba, saboda duk lokacin da ka fadi hakan, kwakwalwarka ta dauka. Zuciyarka ta karba. To fa hakan zata kasance maka.
Mafi girman baiwar da Allah yayi maka shine da ya halicceka dan Adam. Lokaci yayi da ya kamata ka fara amfani da wanna damar indai har kana son samun ci gaba a rayuwarka.
Friday, 25 August 2017
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: