Saturday, 23 September 2017

Ba Zan Taimaka Wa Ma’aikatan Bogi A Karamar Hukumar Kalgo Ba — Namashi Diggi

Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

Shugaban karamar hukumar mulki ta Kalgo, Alhaji Umar Namashaya Diggi ya bayyana cewa ba zan taimaka wa duk ma’aikatan bogi da ke cikin karamar hukumarsa ba a Jihar Kebbi.

Shugaban ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya kammala wata ganawa ta siri da ya gudonar tare da Sarikin Gwandu da daraktocin karamar hukumar Kalgo, iyaen kasa da kuma kansilolinsa da ma sauran masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Kalgo. Taron ya gudona ne a sakatariyar karamar hukumar Kalgo a wannan mako. Tare da cewa, makasudin shirya ganawar domin neman hadin kai don daidaita matsalolin da ya tarar a karamar hukumar tasa.

Diggi ya bayyana wa manema labarai cewa ba zai taba amincewa da duk wani ko wata da a ma’aikatan bogi a karamar hukumar Kalgo ba, ya ce abin takaici ne da ban mamaki kan yadda aikin kananan hukumomi ya lalace saboda son ran da ake sa wa a aiki gwamnati, “Saboda haka ni ba zan yarda da hakan ba a wannan karamar hukumar ba”, in ji shi.

Har wa yau, ya ce “A matsayina na shugaban hukumar Kalgo ba zan amince da wannan tsarin biyan albashin dubu biyar ba da na tarar a lokacin da na karbi madafun iko a hukumar. Ya zama wajibi a matsayina na zababben shugaban karamar hukumar Kalgo, ya zama dole n yi iya kokarina na ganin cewa na dawo da martabar aikin karamar hukumar kamar yadda ka’idar aikin gwamnati take da yaddar Allah”.

Ya ci gaba da cewa, ba zai lamunci yadda wasu ma’aikata ke karbar albashi kawai ba tare da aikin komai ga karamar hukumar. Tare da cewa, “Insha Allah zan gyara wannan matsalar ta yadda kowane ma’aikaci za a dubi matsayinsa na aiki, idon ba a bisa ka’ida yake ba za a daidaita masa zama kamar yadda doka ta tanada”.

Bugu-da-kari ya ce, “Daga wannan wata na Satumba da muke ciki duk wanda ba ma’aikacin halas ba ne a karamar hukumar Kalgo, to ba zai samu albashin wannan watan ba. Domin na fito da wata takarda wadda za ta bayyana ma’aikaci na gaskiya. Lokaci ya yi na samar da canji ga ma’aikatun kananan hukumomin a Jihar Kebbi”.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: