Saturday, 23 September 2017

Gobara Ta Lakume Rayukan Mutum Hudu A Kano

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

Wata gobara da ta tashi a Unguwar Tudun Murtala da ke Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano, ta yi sandiyyar mutuwar mutane hudu tare da jikkata wani jami’in kwana-kwana. Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe goma na ranar Talatar da ta gabata, inda gobarar ta shafe sama da awa biyu tana ci.

Wasu makusantan gidan da gobarar da ta tashi sun bayyana wa LEAERSHIP A YAU cewar, suna zaune suka hangi hayaki na tashi, hakan yasa suka fahimci gobara ce ke ci a wannan gidan, saboda haka suka garzaya domin bayar da gudunmawa.

An ga jama’a sun yi ta amfani da ruwa da kuma kasa don kashe wutar amma idan aka watsa ruwa sai aga kamar kara tunzura wutar aka yi saboda haka aka koma amfani da kasa, bayyanai sun nuna cewa jami’an kashe gobara sun iso wurin tare da ci gaba da kokarin kashe wutar wanda suka dauki lokacin mai tsawo kafin shawo kan gobarar. Kazalika, an kokarin ceto wata karamar yarinya a gobarar wadda daga bisani aka garzaya da ita asibiti saboda yadda wutar ta yi mata illa.

Da yake yi wa wakilinmu karin haske game da lamarin, shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano Mustapha Lurwan, ya ce gobarar ta tashi ne a wani gida da ke unguwar Tudun Murtala a karamar hukumar Nasarawa, gidan matan aure ne mai dakuna hudu tare da shafar wasu gidajen makwabtansu. Shugaban ya bayyana cewar, akwai mutum biyar sakamakon ganin wutar suka shiga cikin daki, sun samu nasarar fito da su tare da gaggauta kai su asibitin Kwararru na Murtala domin karbar magani, amma ya ce bayan da suka koma jami’an lafiya suka shaida musu cewar mutane hudu daga ciki sun riga mu gidan gaskiya.

Haka kuma Mustapha Lurwan ya ce akwai zargin ana sayar da man fetur da kuma man inji a cikin wannan gida, saboda haka suke amfani da wannan dama na ja hankalin jama’a cewar doka ba ta bada damar mutum ya ajiye fetur a gida ba, musamman ganin irin hadarin da ke tattare da hakan a cikin gidajen da mata da kuma yara ke kwana a cikinsa, wanda kuma wannan shi ne makusudin tashin wannan gobara.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: