Saturday, 25 February 2017

Shugaban kasa Buhari ya kira Femi Adesina Karo na Farko

An rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira Femi Adesina, mai bashi shawara na musamman a kafofin watsa labarai da shafukan zumunta.

A cewar Adesina, shugaban kasa Buhari ya kira da karfe 2.43 na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu kuma yaji dadi matuka da yayi magana da maigidansa karo na farko a wata.

Ya rubuta: “Da karfe 2.43 na ranar yau, Asabar, 25 ga watan Fabrairu, 2017, wayana tayi ruri. Wake magana? Tunde Sabiu, mataimakin shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman.

“Rike waya ga shugaban kasa,” inji Tunde.


Kuma cikin wasu yan sakonni, muryar da na sani ta fara magana:

Femi, ya kake?” (Ya fi kirana da Adesina lokuta da dama, amma a yau, ya kira ni da Femi)

Nayi ihu: “Shugaban kasa, nayi kewarka. Ya kake maigida?”


Sai ya fara dariya. Wannan sanannan dariyar. Sannan yace: “Har yanzu ina hutawa. Nagode da ka tsaya tsayin daka a kan makiya.”

Nace aikina ne, shine abunda zan iya yi, tare da kara yadda naji dadin yin magana da shi.

“Ya iyalinka?”


Nace suna lafiya, sannan yace na mika gaisuwarsa a garesu.

“Ina sa ran kara kiranka, “inji shugaban kasa, sannan kuma nayi mai sai anjima, na kara da cewa: “Fatan alkhairi, maigida.”

Wannan lokacin farin ciki ne a gare ni. Sama da wata daya, ina magana tare da mataimaka dake tare da shugaban kasa a Landan. Ko sau daya bance su kai mashi wa yaba, da gangan nayi haka, saboda bawai sai nayi magana dashi bane sannan zan yarda cewa yana raye. Kuma tunda yana cikin hutu ne yana da daman kadaicewa.



SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: