A ra’ayin wasu, kishi na nufin nuna damuwa ko kyashi a kan wani abu ɗaya da mutane fiye da biyu ke amfani da shi, ko suke hankoron kishi.
Wasu kuma sun bayyana kishi a matsayin wani yanayi da mutum kan tsinci kansa na son mallakar wani abu ko zuciyar wani, shi kaɗai ba tare da wani ya samu wannan abin ko kulawar wannan mutumin, ko kuma hankalin mutumin ya fi karkata ga mai nuna kishin a kansa ba.
Idan ka shiga wasu gidajen, za ka ga babu kwanciyar hankali ko haɗin kai tsakanin matan, wani lokaci ma har da ’ya’yansu. Kowace tana ganin ita ta fi cancanta miji ya kula ko ya fi son ta ko ’ya’yanta. Mata ina son mu kara fahimtar wani abu, Hausawa kan ce abin da arziki bai ba ka ba, to tsiya ma ba za ta ba ka ba. Saboda haka me zai hana mu kwantar da hankalinmu, mu yi kishi irin na zamani, wanda ba zai kai mu ga halaka ba?
Abu na farko da ya kamata kowace mace ta nema don samun kyakkyawar rayuwa shi ne ilimi. Duk mace mai ilimi za ta kasance abin sha’awa kuma abin koyi ga kowa. Idan an ce ilimi ba wai ana nufin ilimin zamani kawai ba, a’a, bayan ilimin boko, ya kamata mace ta kasance mai ilimin addini, wanda shi ne gaba a kan komai. Sannan kuma ta kasance mai ilimin zamantakewa da jama’a wato ta san yadda za ta rika mu’amala da jama’a don kauce wa kowace irin fitina.
Hausawa kan ce idan ka san halin mutum, to, sai ka ci maganin zama da shi. Komai zafin kishi da abokiyar zamanki ke da ita za ki iya amfani da iliminki wajen ganin kin kauce wa fitinar da za ta bullo. Idan kina da ilimin boko, zai iya kasancewa ke ma’aikaciya ce saboda haka ba ki da lokacin zama ki biye wa kishiya kuna fitina a cikin gida.
Hakazalika mai ilimin addini ta san irin sharuɗɗan da addini ya gindaya mata game da zamantakewar aure da kuma waɗanda take tare da su. Saboda haka komai zafin kishinta tana iya dannewa don gudun kar ta saɓa wa Ubangijinta, wanda Shi ne Ya ba maza damar auren mace fiye da ɗaya, har Ya jaddada cewa su yi adalci a tsakanin matansu don samun lada da kuma kwanciyar hankali.
Sannan kuma kowane irin zama kuke yi da kishiya, kada ki yarda ta haɗa ki faɗa da mijinki. Za ki ga wani gidan kamar ana zaman lafiya, amma sai kishiya ta rika shirya maganganu don ta ga ta haddasa fitina tsakanin abokiyar zamanta da mijinta. Ko a inda ba a zaman lafiyar ma, kullum burinta shi ne ta haddasa wani abu da zai sa ki ga bakin mijinki.
Ina kira gare ku mata, duk abin da kishiya za ta faɗa miki na ɓatunci game da mijinki, koda kuwa kina ganin kin amince mata, to, kada ki yarda ta ga ɓacin ranki, koda abin ya yi miki zafi a rai, ki daure kada ki bari ta gane, kuma kada ki yi masa maganar a gabanta.
Sannan idan za ki yi masa maganar, ki kasance cikin natsuwa yadda ke da shi za ku yi magana cikin fahimtar juna. Kin ga idan kika yi haka koda abin da ta faɗa da gaske ne yana iya ba ki hakuri saboda shi ma zai ji nauyin yadda kika ɓullo masa.
Ina kuma son ki kiyaye, duk abin da ya faru tsakaninki da miji, to, ku yi ku binne a ɗaki ba tare da kishiyarki ko wani ya fahimci cewa wani saɓani ya shiga tsakaninku ba. Ko fushi yake yi da ke idan kuna cikin jama’a ki saki ranki ki kuma lallaɓa shi cikin wasa da dariya. Yin hakan zai sa shi ma ya sauko daga fushin da yake yi.
Wani babban kuskure da mata kan yi shi ne nuna kiyayya ga ’ya’yan mijinsu. Bai kamata don kuna samun saɓani tsakaninki da abokiyar zamanki sai kuma ki tsangwami ’ya’yanta ba. Ki sani laifin wani ba ya shafar wani kuma waɗannan yara ’ya’yan mijinki ne, idan kuma kina son zaman lafiya, to, dole ki so abin da mijinki ke so.
Ki kuma sani, masu iya magana na cewa ɗa na kowa ne. Ki tattali yaro a duk inda kika haɗu da shi. Ba ki san me gobe za ta haifar ba, ta iya yiwuwa nan gaba ki mori waɗannan ’ya’ya na mijinki fiye da yadda za ki mori naki na cikinki.
Saboda haka ki kasance mai tattalin ’ya’yan mijinki a kodayaushe, ki rika jansu a jiki, ki kuma rika yi musu kyauta da ba su shawarwari masu kyau a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Sannan ki kasance a gaba wajen ganin mijinki na biya wa ’ya’yansa bukatarsu. Hakan zai kara miki kwarjini da daraja a wurin mijinki da kuma ’ya’yansa.
A wasu lokuta da dama, za ki ga mace tana tada jijiyar wuya don mijinta ya hana ta fita amma kuma ya bar kishiyarta ta fita. Tana iya yiwuwa abokiyar zaman taki da ta fita ba da izinin mijinta ta fita ba, ta dai gagare shi ne kawai ya bar ta ta fita ba don son zuciyarsa ba, ki sani maza kan so mace mai kame kanta a cikin gida ba tare da yawan zuwa unguwa ba sai dai idan da wata hujja mai karfi. Ki kuma sani wani lokaci idan mijinki na hana ki fita, yana nuni ne da cewa yana matukar son ki saboda haka yana kishin ki rika fita wasu mazan na ganin ki a waje.
Hakazalika kishin zamani na yi mana nuni da cewa yanzu mata ba su yaji, wato ba su barin gidan mijinsu wai don sun sami saɓani da shi. A maimakon haka mace kan yi kishin cikin gida, wanda ko waɗanda take tare da su a gidan ba za su fahimci wani abu ba. Sai dai a tsakaninta da shi mai gidanta za ta ɗan janye jikinta, ta rika ɗar-ɗar da shi har ya fahimci inda ta sa gaba sannan ya nemi sasanci amma fa ki sani, a nan ina nufin in dai laifin mijin ne shi ne za ki iya yin haka, ba wai a ce ke ce mai laifi ba kuma kiyi saurin fushi ba.
Sai dai ki sani yin hakan ba shi ne mafi a’ala a gare ku ba. Idan mijinki ya saɓa miki, mafi sauki shi ne ki zaunar da shi don ku tattauna, ku kuma yafe wa juna. Kamar yadda masu iya magana kan ce, zo mu zauna zo mu saɓa, saboda haka abu mafi cancanta shi ne a rika hakuri da miji da kuma abokiyar zama.
Hakan shi zai kai ki gacin ribar aure duniya da lahira, kamar yadda akan ce, mahakurci mawadaci.

0 comments: