Sunday, 26 February 2017

Yaki Da Cin Hanci: Adadin Kudaden Da Buhari Ya Kwato - Malami

Malami ya ce ma'aikatar sharia ta kara kudaden shiga na gwamnatin tarayya ta hanyar kwato zambar kudi Naira biliyan 57 da miliyan 9 da kuma Dala miliyan 666 da 6,76,000

-Babban mai gabatar da karana gwamnati tarayya ya fadi haka ne a Abuja ranar Alhamis 23 ga watan Fabrairu yayin da ya ke kare kasafin kudin ma'aikatar shari na 2017 a gaban kwamitin da ke kula da bangaren sharia da hakkin dan adam da dokoki na majalisar dattijai a ginin majalisar dokoki.
Babban mai gabatar da kara na gwamnatin tarayya Abubakar Malami ya ce, an dawowa da gwamantin tarayya makudan kudaden da aka sace a yakin da gwamnati ke yi da cin hanci da rashawa.

Antoni janar kuma ministan shari'a Abubakar Malami mai lambar SAN ya bayyan cewa, yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatin tarayya ya taimaki Najeriya ta hanyar dawowa da tsabar kudi kimanin naira biliyan 57 da milyan 9, da kuma Dala miliyan 666,676.
A cewar wani labari da kafara yada labarai ta PR Nigeria, Malami ya bayyana haka ne a Abuja ranar Alhamis 23 ga watan Fabrairu yayin da ya ke kare kasafin kudin ma'aikatar shari'a a gaban kwamitin shari'a da hakkin dan adam da dokoki a ginin majalisar dokoki.
Malami ya kuma ce, "Naira biliyan 50 tara ce da aka ci kamfanin MTN yayin da aka gano Naira biliyan 7 da dala miliyan 10 a gidajen wasu".

"Sai Naira miliyan 40 da Naira miliyan 50 da aka dawo da su bisa ra'ayin kai, sai kuma wasu Dala miliyan 200, da Dala miliyan 136 da 676,000 wadanda ake shirin shigar da su asusun gwamnatin tarayya, baya ga Dala miliyan 270 wadanda aka gano su a asusun bankunan kasuwanci".

Ko shakka babu tsabar kudi Dala miliyan 9 da 8,000 da aka kwace daga hannun tsohon shugaban kamfanin mai na NNPC Andrew Yakubu na daga cikin kudaden da atoni janar din ya gano.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: