Sunday, 26 February 2017

Dalilai Biyar (5) Dasuke Tabbartar Da Talauci Yafi Yawa A Arewacin Nigeria Inji Sanata Shehu Sani

Manyan dalilai 5 da su ka sa har yanzu Arewancin Najeriya ya fi ko ina talauci - Sanata Shehu Sani
-Shehu Sani, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya dora laifin talaucin da ake fama da shi a Arewacin Najeriya kan attajiran 'yan siyasa.

A cewar sanatan yakin Arewa ya fi ko wanne yanki talauci a kasar nan duk da yawan attajiran da ke yankin.

1. Su na aiki tukuru su na samun kadan

Sanata Sani ya ce, talakawa su na yi mana wahala su yi kokarin zabar mu, amma duk da haka ba abin da su ke samu.


2. A ci moriyar ganga a ya da kwauronta

Ya ce, talakawa da masu bukata ta musamman ana watsar da su bayan kammala zabubbuka.

"Ko yaushe abin da ke faruwa kenan; duk lokacin da mu ke takarar wani mukamin siyasa, mu na nemansu a lunguna da sakuna amma da zarar mun ci zaben, babban abu shi ne yadda za mu kawar da su daga titunanmu".

2. Bara

Ba za ka iya kawo karshen bara a kowane yanki a Najeriya ba ba tare da ka samar masu hanyoyin kyautata zamantakewa da tattalin arzikinsu ba. Haka abin ya ke ko yaushe.


"Bara da zaman banza matsala ne ga tattalin arziki.

"Bara ta kasance babbar matsala a Arewacin Najeriya amma ba za a iya magance ta ba saboda ba a dauki matakan tattalin arziki da za su magance ta ba."

4. Babu taswirar tattalin arziki

"Ba za ka iya yi wa mutane dokar fita daga talauci ba; dole ka shimfida tsarin tattalin arziki da zai taimakawa wadannan mutane su tsaya da kafarsu".

5. Ana ganin talakawa matsala ne.


"Da yawa daga attajiran Arewa su na ganin talakawa matsala ne a al'umma wanda ya kamata kakkabe su. Kuma ba za a iya kakkabe su ba".

Sanata Shehu Sani na kan gaba wajen magana kan sharhi al'muran da suka shafi jama'a tare da gwagwarmaya kare hakkin dan adam tun kafin ya zama dan majalisar dattijai.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: