Wednesday, 1 March 2017

An Gano Asalin Cutar Dake Damun Shugaba Buhari (Karanta Bayanin)

Wata majiya dake kusa da shugaba Buhari ta shaidawa jidan jaridar Sahara Reporters ainihin cutar da ke damun shi shugaban

- Majiyar wadda bata so a bayyana sunan ta ta bayyana cewa Buhari yana fama ne da gyambo a cikin sa da kuma wata irin cuta mai matsala da ake kira 'Crohn's Disease' wadda ake dan gantawa da kumburin yan hanji.
Majiyar ta sake jaddada cewa wannan cutar ce ma ke hana shugaban cin abin ci da kuma rama musamman a farkon shekarar nan.

Majiyar ta shaida mana cewa dama dai a shekara ta 2013 an yi wa Buhari aiki inda aka cire masa wani bangare dake cikin sa.

A wani labarin kuma, tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari ya yabi Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ya ke kokarin ganin ya gyara kasa Najeriya.


Shagari ya ce Buhari mutum ne mai gaskiya, rikon amana da kishin kasa.

Yace kokarin da Buhari yakeyi musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa sannan da seta Najeriya akan tafarkin kwarai abu ne wanda ya cancanci yabo.

Shagari ya kara da cewa dole a jinjina ma Buhari akan yadda ya ke ta kokarin ganin ya farfado da tattalin arzikin kasa Najeriya da irin shirye shirye da gwamnatinsa ta bullo dasu domin samun nasara akan hakan.

Shagari ya fadi hakanne a yayin da yake jawabin murnan zagayowar ranar haihuwarsa a garin Sokoto.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: