Sunday, 5 March 2017

APC na shirin murde zaben 2019 inji Gwamna Wike

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas yayi ikirarin cewa Hukumar zabe ta kasa INEC na shirin murde zabe mai zuwa na shekarar 2019 domin Jam’iyyar APC mai mulki tayi nasara.
Gwamna Wike yace Hukumar INEC mai gudanar da zabe na kasa na kokarin murdiya a zabe mai zuwa domin APC tayi nasara. Gwamnan yace Hukumar ta INEC tayi kokarin murde zaben da aka gudanar kwanan nan a Jihar sa domin APC ta lashe zaben.

Nyesom Wike ya bayyana wannan ne yayin da ya kai ziyar karamar hukumar Etche da ke Jihar Ribas din inda yayi godiya ga mutanen yankin da suka zabi PDP a karashen zaben da aka yi kwanan nan.
Gwamna Wike yace da gan-gan INEC ta ke tura wasu Jami’ai domin ayi murdiya sai dai Gwamnan yace babu wanda ya isa ya ci nasara wajen murde zaben Jihar Ribas. Dan takarar PDP ne dai yayi nasara a zaben Dan Majalisar da aka gabatar kwanan nan din.

Haka kuma da alamu dai bangaren su Sanata Makarfi suna shirin kafa wata sabuwar Jam’iyya mai suna APDP daga cikin PDP. Sai dai Shugaban bangaren na PDP Ahmed Makarfi yace babu shi a cikin wannan yunkurin. Rikicin Jam’iyyar PDP dai na ta kara cabewa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: