A irin sanin da mutane sukayi wa Hamid Ali ba karamin aikinsa bane yace ba zai cigaba da rike hukumar kwastam ba saboda matsawa da majalisa tayi na dole sai ya saka kayan kwastam kafin su saurareshi.
Majalisar dattijai ta kori shugaban hukumar Kwastam Hameed Ali da ga zauren majalisar bayan ya bayyana a gabanta domin amsa kiran da tayi masa.
Mataimakin shugaban majalisar Ike Ekweremadu wanda shine ya shugabanci zaman majalisar yau yace majalisar ba za ta saurari Hameed Ali ba saboda rashin saka Unifom da bai yi ba.
Ko da yake Hameed Ali yace babu wata doka da tace dole sai ya sa Unifom kafin ya tafi wajen aiki.
Sanata Bala Ibn Na’allah ya karyata hakan inda ya karanta masa wata sashe a dokar kasa da ya tilasta wa duk wani ma’aikacin hukumar Kwastam din saka Unifom.
Sanata Olamilekan Solomon (APC-Lagos), Barnabas Gemade (APC-Benue) da Barau Jibrin (APC-Kano) duk sun koka da kin bin umarnin majalisar da Hameed Ali yayi na zuwa ba tare da ya saka Unifom ba.
Daga karshe majalisar ta kore shi sannan ta ce ya dawo gabanta ranar Laraba mai zuwa sanye da Unifom.
Abin lura anan shine, tun da farko Hameed Ali ya nuna rashin gamsuwar sa da neman dole sai ya saka kayan aikin kwastam din.
Yayi kokarin nuna wa majalisar cewa hakan ba shine ya kamata su dage akai ba, ya nemesu da su duba aikin da akeyi a hukumar tun daga zamansa shugaban hukumar.
Duk da nuna musu hakan sanatocin sun kafe akan matsayar su na dole sai ya saka kayan aikin kafin su saurareshi.
Sanin kowa ne dai cewa Hamid Ali mutum ne da yake kwatanta gaskiya a dukkan al’amurorinsa wanda hakan yasa suke da kusanci da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
An shede shi da gaskiya da guje wa abun duniya.
Abin tambaya anan shine mene ya sa majalisa suka da ge sai ya saka kayan kwastam din kafin su saurare shi?
Masu sharhi sun ce a ganinsu kawai ana hakan ne domin a nuna masa isa da iko amma bawai don za ta amfanar da majalisar ko Najeriya da wani abu ba.

0 comments: