'Yan uwana masu karatu, kamar yadda na yi muku alkawari a baya cewa, zan tsakuro muku wani abu mai kama da taɓa-ka-lashe daga cikin rubutun babban marubucin nan Ash-Sheikh Ali at-Tantawi da ya rubuta ƙarkashin waccen matashiya ta sama, a littafinsa mai suna "Az-Zikrayaat" wato 'Tuna Baya'.
A baya
Na Ga ‘Mutuwa’ A Ranar Tunawa Da Shahadar Husaini (R.A) Fitowa Ta 1 - Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, Kano
Ka da ku manta na faɗa muku cewa, ba zan iya kawo rubutunsa yadda yake ba, cike da fasaharsa da taswirarsa, sai dai in kwatanta, domin an ce, 'linzami ya fi ƙarfin bakin kaza'.
Malam dai ɗan asalin ƙasar Syria ne, amma ya yi zaman karatu a Masar, sannan ya koyar a Iraƙi, ya ziyarci wasu ƙasashe dadama, daga ƙarshe ya yada zango a ƙasar Saudiya, a nan Allah ya yi masa rasuwa a shekarar (1999 A.D). A zamansa a Bagadaza ta ƙasar Iraƙi ya fita wata rana inda ya ga 'mutuwa' amma Allah ya kuɓutar da shi, daga baya ya yi rubutu a kan wannan labari, inda yake cewa,
"Ranar Ashura a Iraƙi wata rana ce ta daban. Duk garin yakan koma tamkar ana zaman makoki, kai ka ce, jiya-jiyan nan ne aka kashe Husaini (r), ko kuma ka ce har yanzu Banu Umayya ne ke rike da ragamar mulki; ko kuma wadanda aka kashe Sayyidina Husaini (r) tare da su, su ne a kan kujerar mulki.
Mutane sun manta da cewa, Duniyar fa ta canza, wasu ƙasashe sun gushe, wasu kuma sun kafu, komai a doron ƙasa ya canza akan yadda da yake, kaɗai al'adar waɗannan mutane ne ita ce ba ta canza ba har yanzu, jiya-a-yau.
Mu Musulmi duka muna son Annabi (S.A.W), duk wanda ma ba ya son shi fiye da yadda yake son kansa to imaninsa bai cika ba. Kuma muna son duk mai son Manzon Allah (S.A.W). Kuma jikokinsa Hasan da Husaini suna son shi, don haka mu ma muna sonsu, muna son iyalan gidan Manzon Allah duka, don haka ne ma muke sa su a cikin salatin da muke yi wa Annabi (S.A.W). Amma duk da haka ba za mu taɓa yarda mu aikata abin da Annabi bai yi umarni da aikata shi ba, don kuwa ba za mu saɓa masa ba mu riƙa yin gaban-kanmu. Abin da muka ga wasu mutane a Iraƙi suna yi ya saɓawa koyarwar Annabi (S.A.W) kuma ba zai taɓa amincewa da haka ba.
A wannan rana ta Ashura Abokina Anwar ya buƙaci mu tafi garin Hillah (yanki ne na 'yan shi'a a Iraƙi) yawon buɗe ido. Sai na yarda. Kuma muka nemi wasu ɗalibanmu su uku su yi mana rakiya. A cikinsu akwai wani basamuden ɗalibi, idan na tsaya kusa da shi dakyar kaina yakan gota kwankwasonsa kaɗan, wani lokaci ma nakan tsokane shi in ce masa, wai kai ba ka gamuwa da matsalar iskar shaƙa (Oxygen) a sararin samaniya idan kana tsaye?!. Amma kuma duk da haka yaro ne mai kirki, mai kyawawan halaye, sunanshi Abdullahi Adi. Ka ji sunan shi ma 'Adi' kamar sauron ɓurɓushin Adawa mutanen Annabi Hudu. (A.S). Sauran ɗaliban guda biyu, ɗayansu ɗan Sunna ne, gudan kuma ɗan Shi'a ne.
Kashe Sayyidana Husaini wata mummunar aika-aika ce, e, zan sake maimaitawa, mummunar aika-aika ce, a fahimci hakan da kyau. To fa amma da jimawa wasu mawaƙa da marubuta Adabin larabawa sun yi ta ƙarin gishiri mai yawa a wajen bayanin wannan 'aika-aika' domin sun mayar da ita wani fage na sukuwar dawakan adabinsu, da sakin linzamin waƙoƙinsu. Lalle kam sun yi sukuwa yadda suke so, to amma fa sun lullube gaskiyar al'amarin da ƙurar sukuwar dawakansu.
Waƙi'ar kashe Husaini, waƙi'a ce da ta faru tun shekaru masu yawa da suka wuce. Marubuta iri-iri, kama daga marubutan tarihi da mawaƙa da marubutan adabi da al'adu kowa ya yi ta rubutu a kai, kuma kowa yana zana irin tashi taswirar yadda waƙi'ar ta kasance. Kusan babu wani labari mai sanya idanu su rika kwararo da hawaye da ba a faɓa ba a kai.
Duk wani abu da yake nuna zalunci da rashin imani da ƙeƙashewar zuciya, da nuna rashin mutunci da tumasanci, duk sai da aka tattaro su aka zuba su a cikin labarin wannan waƙi'a. Kai yau da a ce Miyagun mutanen na da aka yi a tarihi irin su, Nero ko Genghis khan, ko ma yahudawan da suka fi su sharri a yau irin su Begin da Shamir, su ne ake ba da labarin an yi musu irin abin da masu ba da labarin waƙi'ar Karbala suke faɗa, to babu shakka sai ka tausaya musu idan ka ji, sai ka jajanta musu a kai. To kuma balle a faɗa maka cewa, duk wannan abu ya faru ne ga 'ya 'yan Nana Fatima, jikokin. Ma'aiki (S.A.W) yaya za ka ji a ranka?!
Wannan shi ne zai sa ka fahimci dalilin da ya sa muke ganin abin da ake yi a ranar Ashura game da Husaini irin wanda ba a yi wa Ali ko Mazon Allah kwatankwacinsa, alhali kuwa sun fi shi daraja nesa ba kusa ba.
Muna tsakar yawo a garin Hillah ne, sai muka gan mu a wani babban fili an zageye shi da katanga, da ƙofar shiga guda ɗaya a buɗe. Sannan muka ji wani sautin rera waƙe mai cike da tausayi yana fitowa daga cikin wannan kango. Muna leƙawa sai kawai mu ga wasu mutane a ciki zaune babu komai na tufafi a jikisu in banda abin da suka rufe al'aurarsu zuwa cibiyoyinsu. Sun bar ƙirajensu tsirara a waje. A tsakiyarsu sai muka hango wani zaune sanye da koren rawani (alamar shi Sayyid ne Ahlul Baiti). Wannan mutum shi ne mai ba da waƙen, sauran jama'ar dake zagaye da shi sahu-sahu suna masa amshi.
Daga nan sai abokina Anwar ya tambaye ni cewa, ko za mu shiga wannan kangon ne? Sai na ce mu tambayi waɗannan ɗaliban domin su ne 'yan gari, su suka fi mu sanin ƙasarsu. Sai suka ce mana kada mu yarda mu shiga. Ai kafin mu ankara shi gogan naka Anwar har ya shige. Daga nan muma muka yanke shawarar mu bi bayansa.
Mu kwana a nan, Saboda haka Ku Karanta Karo na uku a Na Ga ‘Mutuwa’ A Ranar Tunawa Da Shahadar Husaini (R.A) Fitowa Ta 3 - Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, Kano

0 comments: