Tuesday, 22 August 2017

Ta Allah Ba Taku Ba: 'Yan adawa sun fara hurawa Shugaban kasa Buhari wuta daga dawowa

Mun ji cewa an nemi Shugaban kasa Buhari ya bayyanawa 'Yan Najeriya halin rashin lafiyar sa kowa ya sani.
Tarin wasu Jam'iyyun adawa na kasar irin su SDP, ADC, NCP da UDP sun soki jawabin da Shugaban kasar yayi a jiya su kace Shugaba Buhari bai yi wa 'Yan kasar bayani game sa halin rashin lafiyar sa ba da ya dauki dogon lokaci fiye da kwanaki 100 yana jinya.

Tanko Yusuf wanda shi ne Shugaban Jam'iyyar NCP ya soki jawabin Shugaban kasar musamman ganin yadda bai yi magana game da batutuwan da ke tashi ba irin su kiran yi wa Kasar garambawul. Bayan tafiyar Shugaban kasar zuwa Landan dai an tado da maganar yi kasar sauyin tsari.

Labari ya zo mana cewa wasu Jihohi sun shirya biki na musamman dalilin dawowar Shugaba Buhari bayan jinyar rashin lafiya.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: