Wednesday, 16 August 2017

Tirƙashi: Rundunar Ýansanda ta bayyana fuskokin ýan luwaɗi da ýan fyaɗe a Kano (Hoto)

A ranar Talata 15 ga watan Agusta ne rundunar Yansandan jihar Kano ya bayyana fuskokin wasu mutane da dama data kama kan zarginsu da aikata laifukan da suka shafi luwadi da fyade ga kananan yara.

Kaakakin rundunar, DSP Magaji Musa Majia ne ya jagoranci bajekolin ma’aikata miyagun laifukan a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Kaakakin ya bayyana cewa jami’in rundunar tasu sun samu nasarar cafke miyagun mutanen ne a unguwanni daban daban na jihar Kano, inji rahoton majiyar Arewarmu.com.

Wani abin haushi shine yadda Majia ya tabbatar ma manema labaru cewar cikin mutanen da aka kama akwai mutumin daya dibga ma yarsa ciki har sau 3, kuma ana zubarwa, kaico!

Sauran kuma sun hada da mutanen da basa iya fin karfin zuciyarsu, masu aikata fyade ga kanann yara mata, sai kuma yan kuwadi, wanda Kaakain yace cikinsu har da wani Malami.

Daga karshe Majiay ya tabbatar da cewa rundunar ta kammala shirye shiryen gurfanar dasu gaban kuliya manta sabo domin su fuskanci hukunci daya dace da laifukan da suka aikata.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: