Thursday, 7 September 2017

Babbar Magana: Wani Dan Sanda Ya Hallaka Kansa Sakamakon Chanja Masa Wajen Aiki Zuwa Jahar Da Ko Wane Ma'aikaci Ke Tsoro

Rahotanni da ke fitowa daga jihar Ebonyi sun nuna cewa wani 'dansanda Donatus Oyibe ya halaka kanshi ta hanyar fadawa a cikin wata rijiya a unguwar Ukwuakpu na Abakaliki ranar Lahadi da dare yayinda ya je diban ruwa.

Oyibe dan asalin Ndiagu Ishieke ne a karamar hukumar Ebonyi wadda bayanai suka nuna cewa yana ta fama da matsanancin damuwa tun lokacinda takardar canjin wajen aikinsa ya fito zuwa jihar Borno ranar 28 ga watan Agusta.

The Sun ta ruwaito cewa diyar mamacin Ukamaka ta shaida cewa mahaifinta yaje rijiyar domin ya debo ruwa amma da yake bai dawo ba har zuwa tsawon wani lokaci sai aka tafi domin a gani ko miye ke faruwa inda aka sami bokitinsa a bakin rijiya amma ba'a ganshi ba,lamarin da ya sa aka tsananta bincike da ya kai ga gano gawarsa a cikin rijiyar.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: