Saturday, 23 September 2017

Kwastam Sun Gano Masu Shigo Da Maka-mai Nijeriya, Ko Kun San Su Waye?

Daga Mubarak Umar, Abuja da Abba Abubakar, Kaduna

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa ta bayyana cewar ta gano wadanda suke shigo da makamai cikin kasar nan daga Kasar Turkiya.

Bullar wannan rahoton ke da wuya gwamnatocin kasashen biyu, watau nijeriya da Turkiyya suka kira taron gaggawa a Birnin Tarayya Abuja a jiya Juma’a, don samar da mafita wajen magance shigo da makaman ba bisa kaida ba.

Kwanturola Janar na Hukumar, Kanal Hameed Ali (mai ritaya) wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai ya ce, kamfanin Great James Oil Gas su ne suka shigo da makaman.

Idan dai za a iya tunawa, a tun daga farkon wannan shekarar ce, sau hudu ke nan ana shigo da irin wadannan makamai cikin kasar nan ta barauniyar hanya daga kasar ta Turkiya wadda kuma jami’an hukumar suka kama.

Kanal Ali ya ci gaba da cewa, “duk kan Kwantirololi na Hukumar na shiyyar kasar nan, an sanar da su da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana har da na filayen sauka da tashin jirage da sauka da na tashoshin ruwa dake kasar nan da kuma iyakokin kasar nan.

Ya ce Hukumar kuma tana yin hadin gwiwa da Hukumar Jami’an Farin kaya ta DSS da sauran jami’an tsaro na kasa da nu nufin magance shigo da makaman.

Kanal Ali ya ce, “a yanzu an sa ido sosai a tashar jirgin ruwa ta Tin-Can Inland ganin cewar ta zamo ruwan dare wajen shigo da makaman cikin kasar nan.

Ya ce, “Hukumarmu ta kara tasa ido kwarai kan kwantononin da ake shigo da su daga kasar ta Turkiyya. Sakamakon hakan shi ne wanda a yanzu kuke gani a kasa. Jirgin ruwan da ya shigo da mugayen makaman sunansa, ‘M.B Arkas Africa, mallakar wani kamafani mai su na, Hull Blyth Shipping.

Ya bayyana cewar, kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na kayan makaman da aka shigo da su, ba a tantance su ba.

Kanal Ali ya ce, “bincikenmu ya nuna cewar, wasu ‘yan kasar nan marasa kishi su ne kashin bayan shigo da makaman tare da hannun wasu daga kasar ta Turkiyya.”

“Har yanzu ba mu kai makurar wannan ta’asa ba, kuma shin wadanan makaman ana shigo da su kasar nan ce don kasuwanci ko kuwa don a bawa wata kungiya ce ta ta’addanci ko kuwa wata kungiya ma su fafutuka ko kowa masu garkuwa da jama’a?”

Ya ce, har yanzu Hukumar Jami’an Farin Kaya ta DSS nakan gudanar da bincike kan wadannan makaman kuma za ta sanar da mu sakamakon bincikenta.

Har ila yau ya ce, “A bangaren Hukumar mu kuwa, mun fito da tsari, kamar yadda n ayi maku alkawarin cewar z amu kara fadada bincikenmu da zai wuce a iyakar kasar nan.”

Ya ce, “tunda yanzu mun gano kasar da ake shigo da makaman, ba za mu gajiya ba wajen ganin mun kai gindin tushen abin.”

Kanal Ali yace, tuni shugaban kasa Muhamadu Buhari ya yi jawabi akan wadannan makaman a babban taro na kasa kuma an umarci jakadan Turkiyya dake kasar da ya zauna damu, don samar da fita.

Ya ce hukumar ta kara yawan yin zirga-zirgarta a iyakokin kasar nan da nufin kakile shigo da irin wadannan makamai cikin kasar nan.

Koda yake, Kanal Ali ya ki bayyana sunan kwantainar da aka shigo da makaman, duk da kokarin da manema labarai suka yi na neman sani.

Ya yi nuni da cewar akawai bukatar da a samar da na’urori na zamani don saurin gano irin wadannan maggan makamai da ake shigowa da su kasar nan.

A nasa jawabin, Kwantirolan Hukumar na shiyyar tashar jirgin ruwa ta Tin Can Island Bashar Yusuf, ya bayyana cewar a farautar da suka yi ta karshe, sun samu nasarar cafke bindigogi masu sarrafa kansu guda 470.

Tsakanin watan Janairun 2017 zuwa Satumba, Hukumar Kwastam ta samu nasarar kame makamai har sau hudu, wadannan ake shigowa da su ta barauniyar hanya daga kasar ta Turkiya wadda kuma jami’an hukumar suka kama, inda a cikin watan Fabirairu an kama makamai 661, a watan Yuni an kama 440, a kuma cikin watan Satumba an kama 1,100 an kuma kama 470, inda jimlar su ya tashi 2,671.

A wani labarin kuma, Hukumar Kwastam ta samu nasarar kama mutane 28 wadanda ke aiki a Tin-Can Inland da ake zargi da hannu wajen shigo da makaman.

Wannna ya biyon bayan irin tsananin binciken da Kwastam din ke yi na bankado bara-gurbi, wadanda ake amfani da su wajen shigo da kayayyakin aiwatar da ayyukan ta’addanci.

Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaidawa kafar sadarwar NewsRangers cewar, tuni wadanda ake zargin suna tsare inda ake gudanar da bincike, wanda da zarar an kammala za a tasa keyarsu, su da wadanda ke taimaka masu gaban kuliya.

Har ila yau, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Birnin Tarayya Abuja, Mista Sadik Bello, ya ce rundunarsu ta yi nasarar cafke wasu mutum uku da ake zargi da kera makamai a kauyen Shenagu da ke Abuja.

Da yake zantawa da manema labarai, Kwamishinan ya bayyana sunayen wadanda ake zargin da: Philip John, Mista Onyegabueze Okpara da kuma Joseph Bulus.

Ya ce tuni rundunar ta fara bincike kan irin makaman da wadannan mutane suke kerawa da suka hada da manya da kananan bindigu, alburusai, da kuma karamin bom.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: