Wani matashi ya shiga hannun hukuma bayan ya daba ma budurwarsa Kehinde Olomola kwalba a jihar Legas sakamakon rashin girka masa abinci da matar ke yi masa.
An gurfanar da mutumin ne a gaban kotun majitsir dake karkashin jagorancin Alkali Jimoh Adefioye a ranar alhamis 7 ga watan Satumba, kamar yadda kamfanin dillancin labaru ta ruwaito.
Dansanda mai kara, Sufeta Akpan Ikem ya bayyana ma kotu cewar saurayin mai suna Babatunde Adeoye ya tafka ma budurwar tasa aika aikan ne a ranar 1 ga watan Agusta a rukunin gidaje na Obada, dake Unguwar Badagry.
“Wanda ake zargin ya caccaka ma budurwarsa wuka ne bayan da suka fara musu sakamakon rashin girki da budurwar tayi, hakan ya sanya saurayin caka ma budurwar wuka a kafa da hannayen ta.” Inji Dansandan.
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito wannan laifi da mutumin ya aikata yaci karo da sashi na 171 na kundin laifukan jihar Legas, kuma zai iya fuskantar hukuncin shekaru 3 a gidan yari.
Bayan sauraron karar, sai alkali ya dage shari’a zuwa ranar 5 ga watan Oktoban shekarar 2017

0 comments: