Tuesday, 19 September 2017

Yadda Na Zana Taswirar Kasuwar Sabon Garin Kano - Alin Bagadaza

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

A cikin makon da ya gabata ne shugaban kungiyar ‘yan Kasuwar Sabon Gari a Jihar Kano, Alhaji Ali Bagadaza ya bayyana yadda aka tsara ginin kasuwar.

Ya ce, a lokacin mulkin Soja na Janar Sani Abacha, lokacin da Wase yake a matsayin Gwamna a Kano, wannan lokacin ya kira shi akan a tsara ginin Kasuwar Sabon Gari. “Farar takarda kawai aka bani na zana taswirar da a halin yanzu kasuwar ke kanta”. In ji Alin Bagadaza

Shugaban yayi wannan bayani ne a lokacin da Majalisar Matasan Arewa masu kishin zaman lafiya ta karrama shi da lambar Ambasadan zaman lafiya a Kano.

Alhaji Alin Bagadaza ya ce, yau shekararsa 54 a cikin Kasuwar Sabon Gari, wannan ya sa suka san duk abubuwan da ya kamata dan kasuwa ya rike domin cin moriyar sana’arsa.

Ya bukaci kwamitin da aka dorawa alhakin tattara gudummawar taimakon wadanda annobar gobara ta rutsa da su a kasuwanni daban-daban a Jihar Kano da cewa lallai a tabbatar da fito da wadannan kudade a raba.

Alin Bagadaza ya jadadda godiyarsa ga wannan majalisar matasa bisa hangen nesan da su ka yi na bashi wannan lambar yabo, ya ce; za mu ci gaba da yin abin da ya kamata domin ‘yan baya su kwaikwaya.

Shi ma da yake gabatar da na sa Jawabin shugaban kungiyar Majalisar matasan Arewar masu kishin zaman lafiya, Kwamared Yakubu Usaini Takai ya bayyana cewa akwai ka’idojin da kungiyar ke bi domin zakulo wanda za a karrama da wannan lambar ta ‘Ambasadan Zaman lafiya’, ya ce, “ciki akwai sharadin cewa dole wanda za a ba lambar ya kasance dattijon arziki ne wanda ba a samunsa cikin rikita-rikitar kudade, kuma ya kasance amintacce ta fuskar Jama’a, zakakuri wajen kishin ci gaban sana’ar da ya ke, wannan tasa muka zabi baiwa Alhaji Ali Bagadaza da wasu fitattun mutane wannan lamba ta Ambasadan zaman lafiya.”

Kungiyoyi, shuwagabannin al’umma, ‘yan Kasuwa da abokan arziki ne suka yi dafifi a otal din Royar inda aka gudanar da wannan babban taro.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: