Tuesday, 7 March 2017

Dalilan da yasa masarautar Bauchi ta dakatar da Wazirin Bauchi, Bello Kirfi

Masarautar Bauchi ta dakatar da Wazirin Bauchi, Alh. Bello Kirfi daga kujeransa na Waziri.
A takardar dakatarwan da wannan gidan jarida, Premium Times ta gani majalisar sarkin ta ce dabi’u Waziri Bello Kirfi ya na ba masarautar Bauchi Kunya a idanuwar mutane bayan darajar da Allah yayi wa Masarautar.

“ An umurceni da in sanarda kai cewa majalisar sarki a karkashin jagorancin mai martaba sarkin Bauchi Dr Rilwanu Suleiman Adamu ta yi nazarin irin halayyarka na rashin da’a, rashin ladabi da rashin baiwa masarautar Bauchi daraja da mutuncin da Allah ya bata musamman abin takaicin da ya faru ranar a masallacin Juma’a na uku ga watan maris.

Majalisa ta tabbatar baka cancanci shugabanci ba, saboda haka ta ba sarki shawara, kuma ya amince tare da umarnin dakatar da kai daga Wazirin Bauchi/Dan majalisar sarki nan take.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: