Fadar shugaban kasar Najeriya ta kara jaddada irin muhimman manufofin shugaba Buhari musamman ma wajen yaki da cin hanci da rashawa inda a cikin satin nan ne ma suka zayyan irin kudurori da manufofi 10 da gwamnatin ta dauka don kawo karshen cin hanci da rashawa.
Manufofin dai an bayyana su ne a ranar Alhamis din da ta gabata a wurin wani taron da aka gabatar wanda kwamitin nan dake ba shugaba Buharin shawara kan yaki da rashawa ya shirya a Abuja.
Ga dai manufofin na har 10:
1. Kaddamar da shirin binciken kwakwaf watau The Presidential Initiative on Continuous Audit (PICA): Bayan kaddamar da wannan shirin ne dai sai gashi an bankado ma'aikatan boge har 53,000 wadanda ake biya albashi.
2. Gyara a fannin kasafin kudi: Yanzu haka dai gwamnati ta yi gyara musamman ta yadda ake yin kasafin kudi wanda ada yake cike da aringizo.
3. Kaddamar da asusun bai daya watau TSA: Tun bayan da aka kaddamar da wannan shirin a 7 ga watan Agusta na 2015, yanzu haka dai gwamnati ta yi nasarar rufe asusu a bankunan kasar nan da suka kai 20,000 inda kuma aka samu makudan kudade.
4. Yin anfanin da lambar tantancewa ta bai daya na Bankuna watau BVN: ita ma wannan yayi matukar anfanin musamman ma wajen biyan albashi yayin da aka gano wasu ma'aikatan da su ka kai yawan 53,000 da suke ansar albashi da asusu da dama.
6. Shiga yarjejeniyar 'Gwamnati a fai-fai' watau Open Government Partnership (OGP): Gwamnatin dai ta shiga wannan yarjejeniyar ne a watan Yulin da ya gabata inda yanzu haka ta kasance ta 70 cikin wadan da suka shiga.
7. Bayar da tayin 'budaddiyar gwamnati ga jihohi': Gwamnatin tarayya ta bayar da tayin shiga budabbiyar gwamnati ga jihohin kasar nan musamman ma wadan da ke bukatar tallafi daga wajen ta.
8. Bayar da lada ga wanda ya bankado bayanin sirri: Wannan sabon salon dai tuni ya fara aiki musamman ma ganin yadda aka fara gano makudan kudade daga wadanda suka sace.

0 comments: