Idan ba ayi wasa ba rikici na iya barkewa a Majalisar kasar nan saboda yadda ake gudanar da sha’anin kasafin kudin a boye ba tare da su kan su ‘Yan Majalisar sun sani ba.
Ana dai gudanar da harkokin cikin Majalisa ne ba tare da kowa ya san abin da ke faruwa ba; kama daga kudin da ake rabawa ga ‘yan majalisu domin su yi aiki a yankin su zuwa sauran harkoki kamar yadda wata Jarida ta gano.
Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume ya kalubalanci Bukola Saraki kwanaki da ya bayyanawa jama’a kasafin kudin majalisar domin kuwa babu wanda ya san abin da ke faruwa. Har yanzu dai ba za a iya ce maka ga abin da ke kunshe cikin kasafin kudin majalisar ba.
‘Yan Majalisun dai suna cewa shugabannin su ne kadai da kuma akawun Majalisar suka san irin wainar da ake toyawa game da harkar kudin Majalisar, har sauran masu rike da makamai dai ba su san abin da ke cikin kundin kasafin kudin Majalisar ba. Yanzu haka dai ana kara hurawa shugabannin wuta da su bayyanawa duniya kasafin kudin majalisar.
Kwanan nan aka aika wani tsoho a matsayin Jakadan kasar zuwa ga Sanatoci domin su tantance sa. Ko da Dattijon ya hallara gaban masu tantancewar sai wani Sanatan Jihar Legas Gbenga Ashafa ya nemi tsohon ya karanta taken kasar. Nan fa wannan tsoho mai sama da shekaru 80 a Duniya yace ba zai rera taken ba, hakan kuma aka kyale sa.

0 comments: