Hukumar yaki da almundahana da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, reshen yankin kudu masu arewa, wato yankin kabilar Ibo ta tabbatar da kwato Naira miliyan 553.77 daga wasu gurbatattun yan siyasan yankin.
Shugaban EFCC a wannan yankin, Johnson Babalola ne ya bayyana haka a ranar Talata 15 ga watan Agusta a garin Enugu inda ya bada bayanai dangane da ayyukan hukumar, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.
Babalola yace kudaden na daga cikin wadanda yayan jam’iyyar PDP suka yi watanda dasu domin yakin neman zaben 2015 daya gabata, inda yace:
“Mun samu nasarar kwato naira miliyan 300 a jihar Ebonyi, miliyan 82.5 a Abia, sai kuma miliyan 60 a jihar Enugu, kuma muna dakon rahoton bincike daga jihohin Imo da Anambra.”
Majiyar Arewarmu.com ta ruwaito shugabana yana fadin zasu gurfanar da kafatanin ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, na jihar Imo, Anambra da Enugu da aka kama da laifi gaban kotu don, kamar yadda yace sun samu koke guda 503 daga jama’a.
Cikin wadannan koke, EFCC ta gudanar da bincike akan 333, yayin da mika guda 88 gaba kotuna daban daban, sa’annan zuwa yanzu sun samu nasara akan shari’o’i guda 5.
Daga karshe, Mista Babalola yace yakid a rashawa a Najeriya, musamman kwatar kudaden gwamnati daga hannun barayi ba karamin aiki bane, saboda tsatstsaran tsari barayin suke yi kafin suyi sata.

0 comments: