Wednesday, 16 August 2017

Kalmomi 5 da Bature ya samo daga harshen Najeriya

Kamar kwanakin baya wannan karo mun kawo maku jerin wasu kalmomi da aka aro daga harsunan Najeriya zuwa Ingilishi.

Kadan daga ciki:

1. Okra

Asali wannan kalma daga harshen Ibo aka dauko ta. Turawa na kiran kubewa da Okra a harshen Ingilishi.

2. Bogus

Asali wannan kalma daga Hausa ta fito kamar yadda masana su ka fada. Yanzu Bature kan yi amfani da wannan kalma.

3. Juju

Asali ma dai Juju kalmar daga Najeriya aka dauko ta. Juju na nufin abin da ya shafi Aljanu ko kuma wata rawa ta mutanen mu.

4. Tango

Haka dai kalmar Tango asali daga harshen Ibibio na mutanen Kasar Kudu ta fito wanda ainihi rawa ne na mutanen Yankin.

5. Buckra

A yaren mutanen Efik, Buckra na nufin Bawa wanda Turawa su ka ara su ke kiran bakin mutum ko kuma Talaka farin fata.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: