Friday, 18 August 2017

Dalilin da ya sa nake boye wasu abubuwan da suka shafe ni – Nafisa Abdullahi

Shahararriyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi ba da tsokaci kan halin da masana’antar shirya fina-finai ke ciki sannan kuma tayi wa masoyanta albishir kan sabon shirinta dake kan hanya.

A cewar jarumar tayi shiru kwana biyu ne domin ta mayar da hankalinta kan sabon fim din da take kan shiryawa a yanzu.

Inda ta bayyana cewa duk wani mai shirya fim yana bukatar nutsuwa domin yin nazari akan abu mai kyau, ta yadda fim dinsa zai yi saurin karbuwa a gurin al’umma.

Nafisa ta ce a yanzu haka tana da fina-finai da dama wadanda aka kawo mata labarin su amma ba lallai ne tace eh ko a’a ba saboda a cewarta komai na tafiya ne bisa tsari. Sannan kuma ba komai ne zata bayyana ba dalla-dalla a halin yanzu.
Da aka tambayeta kan lokacin da zasu saki fim din, jarumar tace bazata bayyana ba amma dai suna aiki tukuru don ganin sun kayatar da jama’a.

Jarumar ta ce ba yanzu zata bayyana ba tukuna. Tace tana da dalilanta na boye wasu abubuwan da suka shafi lamari irin wannan kafin a kammala. A wasu lokutan, idan ka bayyana abu, a karon farko sai ka ga ka ragewa mutane karsashi.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: