Kaakakin majalisar wakilan Najeriya, Honorabul Yakubu Dogara ya tabbatar da samun lafiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yace Buhari ya murmure sosai da sosai.
Kaakakin ya bayyana haka ne ta shafinsa dake kafar sadarwar zamani ta Twitter, jim kadan bayan wata ziyara da ya kai birnin Landan tare da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki inda suka samu ganawa da Buhari a ranar Alhamis 17 ga watan Agusta.
Dogara yace yayi farin cikin ganin shugaban kasa ido da ido, sa’annan ya bukaci yan Najeriya dasu cigaba da yi masa addu’a don ganin ya cigaba da daurewa cikin koshin lafiya.
Yakubu Dogara ya kara da bukatar yan Najeriya dasu dage da addu’a domin samun daman dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari gida Najeriya don cigaba da tafiyar da kasa.
Arewarmu.com ta ruwaito shi yana fadin “A yau mun ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari, naji dadin ganin yadda yake samun sauki. Ina shawartar yan Najeriya dasu cigaba da addu’a a gareshi har sai ya dawo lafiya.” Inji Dogara.

0 comments: