Tuesday, 29 August 2017

Kaico - An kama mai yin farfusu da kayan cikin dan'adam

Rundunar 'yan sanda na jihar Rivers ta kama wani matashi Roland Peter wadda ya shahara wajen sace mutane bayan ya kashe su sai ya sassare su yayi farfusu da sassan kayan cikinsu.
An damke Roland Peter ne yayin da yake shirya wa 'yan kungiyarsa farfesun anta da hanjin wani Fasto mai suna Samuel Okpara da suka saceshi,suka kashe shi kuma suka gundule kansa a garin Ahoada na karamar hukumar Ahoada ta kudu..

Bayanai sun nuna cewa shi wannan talikin shine mai dafa naman wanda suka sace suka kashe ta hanyar shirya farfesun kayan cikinsu da faten ayaban flanten,bugu da kari shi ne ke ajiye bindigogin 'yan kungiyar karkashin jagoransu wadda ake wa lakabi da High Tension .

Kwamishinan 'yansanda na jihar ta Rivers Mr. Zaki Ahmad ya shaida wa manema labarai cewa wanda ake tuhumar yana cikin wata kungiya da suke addabar mutane musamman al'umman karamar hukumar Ahoada ta kudu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: