YERIMA USMAN SHETTIMA shi ne shugaban kungiyar Hadakar Matasan Arewa, wacce a kwanakin baya ta bayar da wa’adi ga ’yan kabilar Ibo da su fice daga yankin Arewa nan da ranar 1 ga Oktoba, 2017 sakamakon yadda su ka zargin Ibon, a karkashin jagorancin wani matashi, Nnamdi Kanu, da nuna kiyayya ga zaman tarayyar Nijeriya, inda su ke gwagwarmayar neman ballewa daga kasar, domin su kafa ’yantacciyar kasar Biyafara.
Editanmu, NASIR S. GWANGWAZO, ya samu tattaunawa ta musamman Shettima, don jin ta bakinsa kan wannan mataki su ka kauka. Amma ya fara da neman sani ko wane ne wannan matashi Yerima Shettima. Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance:
Shin wane ne Shettima?
wSunana Yerima Usman Shettima, ni mutumin Zariya ta jihar Kaduna ne, ni kuma shugaba ne na kungiyar hadin kan matasa ta Arewa ta kasa. Na fara gwagwarmaya tun fiye da shekara 18 da su ka wuce, wato tun lokacin mulkin soja a na gwagwarmaya da ni a karkashin kungiyar NADECO da kungiyoyi daban-daban. Wannan ya biyo bayan tun Ina makaranta Ina yin kungiyar dalibai har na fito. Har ma lokacin mulkin Obasanjo a 2001 a ka samu rashin fahimta tsakanin Arewa da kudancin Nijeriya, wanda a ka hada wata kungiya mai suna OPC.
To, sakamakon wannan kungiya ne su ma dattawan Arewa su ka ga cancantar ni kuma na zama shugaban matasa, don a sami daidaita tsakanin matasan Nijeriya da kuma daidaita tsakanin Kudu da Arewa, musamman ’yan Neja Delta da MOSSOB, wato Inyamurai kenan. A lokacin akwai shugaban kungiyar, wato Alhaji MD Yusif, tsohon shugaban ’yan sanda na kasa da su Sunday Awoniyi da Dan Masanin Kano da sauransu. Ni a ka dauko a ka dora a matsayin shugaban kungiyar matasa, kuma na rika aiki har a ka samu mu kai inda mu ka kai yanzu.
A na cewa, ’yan Kudu da yawa sun a raina ’yan Arewa saboda karancin ilimi, wanda a ke ganin hakan na hana matasan Arewa yin irin wannan gwagwarmaya. Shin kai ka yi wani ilimi ne mai zurfi?
To, b azan ce na yi ilimi mai zurfi ba, amma zan zan gaya ma ka abinda za ka iya kwatantawa. Ka fa dai na farko, Ina da difloma a Political Science (siyasa), Ina da B Sc (digiri) a Public Administration, kuma har yanzu Ina tunanin zan koma na kara karatu.
To, ga abinda ya taso
yanzu ya na nema ya yi zafi har kungiyarku ta bai wa ’yan kabilar Igbo wa’adin su bar Arewa nan da 1 ga Oktoba, 2017. Shin me ya sa ku ka dauki wannan mataki, wanda a ke ganin ya saba wa ’yancin zamantakewa a kundin tsarin mulkin kasa?
To, ka san kowa ya na da yadda yak e kallon abu da kuma yadda mutane su ka tunani a kai. Wannan dai yunkuri das u Inyamurai ko kuma n ace Nnamdi Kanu ya ke yi ba sabon abu ba ne, kuma dokokin duniya sun bada dama wata kungiya ko wani mutum ya ce ya na so ya fita daga Nijeriya. Ita gwamnatin Nijeriya ta san da haka, saboda ta na daya daga cikin kas ashen da su ka sa hannu a Majalisar Dinkin Duniya cewa, idan wani yanki ko wata al’umma ta ce ta na so ta fice daga kasa, a bar su.
To, amma wani ikon Allah tunda Nijeriya ta sa hannu a can, maimakon su yi wani tanadi a dokokin cikin gida cewa, idan wani ya ga dama ya na so zai tafi a yi ma sa wani tanadi na yin ko da kuri’ar raba gardama ne, sai ya zamana kundin tsarin mulkin Nijeriya kuma bai yi wannan tanadi ba. Matsalar kenan. Tun shekara 50 da su ka wuce lokacin da a ka kashe ma na shugabanninmu su Abubakar Tafawa |alewa da su Sardauna har kullum mu na samun wannan barazana ta za su balle.
Har bayan ma an yi wannan yakin na Biyafara an dawo an zauna, an yafe mu su an karbe su a Arewa, an mayar mu su da dukiyarsu, kullum su ka tashi sai su zagi Bahaushe ko su yi ma na kudin goro gabadaya; su ce ma ko ba mu da ilimi ko jahilai ne.
To, su iyayenmu da ya ke su na da al’ada ta hakuri da yakana, juriya da dangana, sai su ka yi amfani da wannan dammar, inda babu wanda su ke wulakantawa kamar mutanenmu na Arewa. To, ka san ita rayuwa ta na canjawa. Ba za a iya cigaba da zama a haka ba. Abinda a ka yi da, ba za a yi shi yanzu ba.
Ka ga farko, da yawanmu gogaggu ne. na biyunsa, mun yi karatu. Na ukunsa kuma babu inda doka ta bada dama cewa a kaskanta ka ko mutum ya wulakanta ka haka kawai don ya na takamar ka na da kawaici. Akwai inda doka ta ce ka fito ma sa. Sai mu ka ga cewa, idan mu ka kai kara ma, gwamnatin Nijeriya ba wani abu za ta yi ba. Idan gwagwarmaya a ke Magana, shi wannan Nnamdi Kanun yaro ne karami a wajena! Ubangidan shi ne sa’ana. Tare mu ka taso.
Idan a ka samu wata hatsaniya mu na mu’amula da shi. Ina kiran sa kai-tsaye, kuma kowa ya san da wannan tarihin. Duk lokacin da a ka samu wata barazana da a ke yiwa mutanenmu a bay azan kira shin a ce ma sa a na yiwa mutanenmu barazana a Imo ko a Anambara ko a ina, kuma zai ce haka ba za ta sake faruwa ba. Ni ma idan wata barazana ta faru ga mutanensu a nan Arewa, zai kira ni, kuma Ina daukar mataki, saboda ni kadai na ke da kungiyar matasa ami shugabaci a kowacce jiha da sauran sassan kasar. Na kafa kungiyar ne saboda gudun abinda zai je ya dawo.
Duk irinsu Asari Dakubo da su Gani Adam duk na samu alaka das u saboda kare hakkin bil adama. Duk dan Arewa day a zauna a Kudu ya san ni, saboda halin da su ka tsinci kansu a lokacin OPC, domin fitar da su a ke yi a na yanka su. Allah Ne kuma ni ne sanadiyya dakatar da wannan abu. Ka ga gwagwarmaya ba sabon abu ba ce gurina.
Wasu na ganin cewa, ku na samun daurin gindi daga shugabannin Arewa ta karkashin kasa, duk da cewa, a fili su na fitowa su ce ba ku kyauta ba da ku ka ce Igbo su bar Arewa.
To, wannan bai zama laifi ba, idan sun yin, amma kuma babu hakan. Ka ga ai duk tsagerancin da yaron nan Kanu ya ke yi, ba a taba yi ma sa magana ba, sai a ka ga zahiri mun fito za mu dauki mataki. Shi ne shugabanninsu su ka fara fitowa su na cewa ba su tare da shi. Sai da su ka ga wuta ta yi wuta, mun ce mutanensu sai sun bar ma na yanki. Don haka abinda mu ka yi, idan dai mutum ya na kishin Arewa ya san daidai ne.
Saboda haka babu mamaki dattawanmu sun ga cewa ya dace a ba mu goyon baya ko dab a za a ce a na tare da mu ba. Amma a gaskiya babu wanda ya sa mu, ba mu yi shawara da kowa ba kafin mu dauki mataki. Idan akwai wani dattijo ma day a fito ya goya ma na baya, shi ne a lokacin da mu ka yi wannan furucin shi ne Farfesa Ango Abdullahi. Shi ne bai yi shawara da mu ba kuma ba tare da ya gan mu bay a fito ya ce wannan abinda yaran nan su ka yi sun yi daidai. Sai kuma yanzu da a ka fara samun wasu su na fitowa su goyi da bayanmu.
To, kai a kanka wasu na cewa, tunda sunanka akwai Shettima a ciki, watakila asalinka ka fito daga yankin Maiduguri ne, inda a ke ta fama da yakI da ’yan tayar da kayar baya na Boko Haram. Don haka ba abin mamaki ba ne don an gan ka ka na janyo tada kura.
A gaskiya ni ba mutumin Maiduguri ba ne. Kusan in ce ma ni ban ma taba zuwa Maiduguri ba sai bana (2017) lokacin da wasu kungiyoyi su ka nemi da na je kan irin wadannan rigingimu, domin a samu zaman lafiya. Amma ni mutumin Zariya ne. Kakata, wacce ta rike ni, ita ce ta saka mi ni sunan mahaifinta Shettima, saboda asalinta mutuniyar Maiduguri ce. Amma ni ba ni da wata mu’amula da Maiduguri a kan waccan rigima. Ni mutumin Zariya cikin birni kuma gidan Bugu.
Kuma Ina so mutane su sani cewa, wannan abinda mu ka yi, ba ni kadai na yi shi ba; kungiyoyi ne guda 16 mu ka hadu mu ka yanke waccan shawara ta bayar da wa’adi ga Inyamurai, don mu nuna mu swu cewa mu na da asali kuma abinda iyayenmu su ka shanye mu ba za mu shanye ba, domin zamani ya riga ya zo. Mu ba mu nuna ba ma son Nijeriya kamar yadda su ka nuna ba, amma kuma ba za mu yarda da cin kashi ba. Yaki su ke so, mu kuma ba ma son yaki. Maimakon a yi yaki, sai mu ka ce tattara su koma can yankinsu, su je su yi Biyafaransu, in ya so mu su bar mu mu zauna lafiya da sauran ’yan Nijeriya ’yan uwanmu.
To, ku kun yarda a balle Biyafara daga Nijeriya kenan?
Wallahi idan su na son tafiya, in shi ne mafio alheri, gara su tafi. Idan kuma su na son zama a Nijeriya, to su tabbatar ma na cewa za su zauna lafiya da kowa. Shi ya sa sakamakon haka mu ka nuna mu su cewa ba za mu dauki doka a hannunmu ba. Shi ya sa mu ka rubuta wasika ga shugaban kasa na rikon kwarya a kwanaki kuma mataimakin shugaban kasa da gwamnonin Arewa da Sarkin Musulmi da duk manyan nan, babu wanda ba mu zauna da shi ba. Haka kuma mu ka rubuta takarda ga Majalisar Dinkin Duniya, wanda yanzu haka ma za mu je can Amurka nan da ’yan kwanaki kadan, saboda mu tabbatar mun gabatar da kararmu gare su, saboda na farko mu na so su nuna wa duniya cewa, yaron nan Kanu dan ta’adda ne sakamakon irin kalamansa da kuma makamai da ya ke nema, don ya haddasa yaki a kasar nan.
Na biyunsa kuma shi ne, a ja hankalin ’yan majalisar Nijeriya da gwamnatin Nijeriya a kan su yi gaggawa su bude wani kudiri a kundin tsarin mulki wanda zai iya bada damar a aiwatar da kudirin da Nijeriya ta sanyawa hannu na bada damar barin kasa ta hanyar kuri’ar raba-gardama. Saboda haka mu na kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Nijeriya ta bude damar ’yancin ficewa daga yankin kasar cikin lumana kamar yadda Inyamurai su ke nema.
To, ai su Igbo a na ganin su na zargin Arewa da cewa, ba su iya bada kowacce gudunmawa ta fuskar tattalin arziki, illa dai yankin ya zama kaska ne kawai, rabi mai jini!
Wannan wata magana c eta zautuwa da hauka. Duk wanda ya ce Arewa ba ta bada gudunmawa, ai bai ma san kasar ba kenan, domin a yau idan Arewa ta balle ta fita daga Nijeriya, to ai ba kasar ma gabadaya kenan. Na biyu kuma su Inyamuran me su ke tsinanawa Nijeriya ne, in banda tsiya da sakarci..? Inyamurai ba su da mai! Idan akwai masu mai ma, ai Neja Delta ne, su kuma ba kasar Inyamurai su ke ba. Kudu maso Kudu ne! kuma shi ma man ai ba na Neja Delta ba ne, saboda na Nijeriya ne. ko kafin a sami man ai an sami arziki na noma a Arewa, wanda a ka yi amfani da shi a ka hako man ba tare da an ce ai arzikin noman na Arewa ne kawai ba. Don haka ba za a kashewa Kudu a hako mai ba.
Shin idan yankin Biyafara zai balle babu Neja Delta a ciki?
Wannan ai hauka ne! Babu Neja Delta, domin ba su da alaka. Amma a haukansu ma har da wani yanki na Arewa, saboda babakere! Wannan abu ba za su kai labara a kansa ba, domin hark ace ta zama ta mai shan kwaya! Mu na da tarihin cewa ya na shan kwaya shi da Fani Kayode. Ai komai ya sa su ka zama abokai a fursuna ba sai don shan kwaya da koken! Shi ya sa tasu ta zo daya!
To, a zaman da ku ka yi da mataimakin shugaban kasa, kafin Shugaba Buhari ya dawo daga jinya a Landan, da kuma Sarkin Musulmi da shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, shin me su ka ce da ku?
Rarrashin mu su ka yi a kan kada mu yarda a tada hankali har a kai ga zubar da jini ballantana asarar rayuka. Ka san da ma mu kullum shugabanninmu na Arewa su na da halin juriya da dattaku. Mu kuma mu na da biyayya, amma mun nuna mu su cewa, lallai a taka wa Inyamuran da ke ci ma na zarafi burki, domin mu ma mu na da abokai a cikinsu!
Sunday, 17 September 2017
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
RELATED STORIES
Sabon gwamnan Nasarawa ya yi wasu muhimman sabbin nade-nade Sabon gwamnan Nasarawa ya yi wasu muhimman sabbi
Kwace akwatin zabe: Sojoji sun sha alwashin bin umarnin Buhari su bindige mutumKwace akwatin zabe: Sojoji sun sha alwashin bin u
Sakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe da BornoSakamakon zabe daga jihohin Kano, Adamawa, Yobe d
Babbar magana: Rundunar soji ta gano sabuwar kungiyar ta'addanci a arewa, hotuna Hukumar soji ta bayyana cewar ta yi nas
Jam'iyyar PDP ta bukaci INEC ta haramtawa Buhari shiga zaben 16 ga watan FabreruJam'iyyar PDP ta bukaci INEC ta haramtawa Buhari
Jaddawalin Manyan 'yan siyasa 6 da gwamnatin Buhari ta daure [photo]Jaddawalin Manyan 'yan siyasa 6 da gwamnatin Buha
0 comments: