Wakilinmu ya labarto cewar wadansu almajirai biyu, Hassan Usman dan 11 da Sa’idu Muhammad mai shekaru 10 a duniya. A ranar Larabar nan da ta gabata ne su ka ketare rijiya da baya a lokacin da su ka samu gudunmawar jama’a daga wani matashi da a ke zargi da niyyar kasha su har lahira mai suna Usman Adamu Aliyu dan shekara 19.
Almajiran dai duka mazauna unguwar Ibrahim Bako ne da ke kan hanyar Gombe a cikin garin Bauchi, inda su ke karatun almajiranci a hannun Malam Umar Muhammad Ladan. Kazalika kuma da wanda a ke zargin ya yaudare almajiran zuwa farfajiyar madatsar ruwa ta Gubi-Dam, inda ya yi niyyar aikata wannan mummunan aiki na kashe yaran.
A zantawarsa da Arewarmu.com A Yau Lahadi shugaban ’yan sintiri na Garu Security Guards ta Jihar Bauchi, Malam Dawa Ya’u Felu, wanda kuma dakarunsu ne su ka yi nasarar kamo wanda ake zargin ya shaida mana cewa, wani manomi ne ya kai rahoton aukuwar lamarin wajen Sarkin Ciro inda shi kuma Sarkin ya sanar da jami’ansu “Manomin ya gano wani yaro na gudu inda ya ke neman dauki ya na cewa ga wani zai kashe shi. Isarmu wajen ke da wuya mu ka samu manomin ya yi kukan kura ya kame shi wannan matashin”.
Ya ci gaba da cewa, a sa’ilin da su ka kawo matashin zuwa ofishinsu don gudanar da bincike matashin ya amsa da kansa cewa halaka yaran ya ke son yi.
“Ya ce mana shi yaron ya yi ma sa laifi na rashin kunya ne, inda ya samu wani abokin sai shi abokin nan nasa mai suna Mubarak ya ce ma sa ai shi da man ya na son sassan mutane, ya ce ya saba ko ya jefa mutum a ruwa ko kuma ya cire sassan jikin mutum. Don haka ya je kawai ya ciro masa kan yaran domin ya huce fushi,” in ji Dawa Felu.
Ya kara da cewa sun kimtsa da shi Mubarak din ne domin ya kawo masa kan yaran wanda ba su kai ga sanin me zai yi da kan yaran biyun ba. Ya ce da bakinsa ya shaida wa wasu ‘yan jarida cewar kashe yaran ya ke son yi.
“Allah Ya sa almajiran biyu su na da nisan kwana a duniya lokacin da shi Usman Adamu Aliyu (wanda a ke zargi) ya yi niyyar aikata aika-aikar da ya kuduri aniyar yi. Daya daga cikin almajiran, Sa’idu Muhammad ya tsalla kururuwar neman tallafi, domin neman taimako gaggawa. Yayin da ya ga an ma ka wa dan uwansa dutse a tsakiyar kansa. Al’amarin da yajo hankalin jama’a daga wani bangaren na farfajiyar madatsar ruwan na Gubi domin kai wa almajiran gudummawar gaggawa,” in ji shugaban.
Ya ce, sun yi amfani da salon a dabara wajen tabbatar da kuma kamo wanda su ka kimtsa kisan yaran da shi. “Mun sanya shi ya kira shi Mubarak din wani mazaunin unguwar Kandahar a nan Bauchi ne ya shaida masa cewar ya kammala aiki, sai shi wanda ya sa shi aikin, ya ce ma sa yanzu ya yi nisa don haka ya boye masa kan yaran idan ya dawo zai amsa. Amma mun bi salon dabara ne ba mu ce ma sa ya nuna mun kama shi ba. shi Mubarak din ya ce wa Usman ya ajiye ma kan zuwa gobe washe garin ranar da a ka kama shi,” in ji shugaban ‘yan sintiri na Garu .
Ya kara da cewa, ya zuwa lokacin ne kuma su ka mika wanda su ka kaman ga ’yan sanda, domin gudanar da binciken musamman a kansa.
Wannan aniya dai ta Usman Adamu Aliyu ba ta kai ga samun nasara ba, inda ka kamo shi a lokacin da ke niyyar aiwatar da mummunar manufar tasa ta halaka yaran. Yayin da a ka tusa keyarsa zuwa ga ofishin Garu Security Guards ta jaha karkashin shugabancin Malam Dawa Ya’u Felu.
Daga basani kuma jami’an Garu Sikuriti su ka hannata shi zuwa hukumar ’yan sanda, domin gudanar da bincike.
Umar Muhammad Ladan shi ne malamin wadannan almajiran. Ya shaida wa Arewarmu.com A Yau Lahadi cewar almajiran nan su na dan gudanar da aikace-aikace a gidan su Usman (wanda a ke zargi), domin neman dan abun kaiwa bakin salati.
Ya ce, ya na da almajiran 150 da su ke karatu a karkashinsa, ya kuma bayyana cewar su na gudanar da harkokinsu ba tare da wata matsala ba.
“Usman Adamu Aliyu dai, kamar yadda ya yi ikirari ya na zargin daya daga cikin almajirin ne, Sa’idu Muhammad, da yi ma sa kazafin satar ragon mahaifinsa, ya tafi da shi wani wurin da ba a fayyace ba, ya sayar da ragon, wanda wannan kazafi ya bata wa Usman rai. Amma mun sasanta su har na tambaye shi ‘ya hakura?’ ya ce min, ‘eh’, ya kuma ce gobe yaran su zo zai ba su kayan sawa,” in ji Malamin.
Malamin na almairan ya ci gaba da cewa, “Bayan yaran sun tashi karatun safe, kuma su ka tafi kalacen dan abun da zasu kai baka. Bisa al’ada sukan dawo makaranta a kan lokaci, amma da maraice ta yi ba mu ga yara ba; shi ne nasa wasu yaranmu su dudduba su ko za su gansu”.
“Zuwa magariba sai a ka buga mun waya, a ke shaida min halin da almairai na biyun su ke ciki. To, ka ji abun da ya faru kenan. Shi ne wnnan matashi mai suna Usman ya dauki almajiran ya je ya kaisu daji yana mena ya kashe su”. In ji Malam Umar
Malam Umar Muhammd ya ce, a bisa dukkanin alamun da su ka gano kasha su har lahira matashin ya nemi yi “domin wallahi a bisa abun da ya faru na dukansu da dutse, ya na nema ya halaka su ne. Domin wadannan yaran ba za su iya zuwa wajen da shi Usman din ya kai su ba, hasali ma ni kaina ban taba sanin wannan waje ba sai yau yau da wannan al’amarin ta auku da almajiraina.wallahi ban taba zuwa wannan wuri ba.”
Haka zalika ya bukaci dukkanin wadanda abun ya shafa musamman jami’an tsaro da su tabbatar da hukuntawa gami da gudanar da muhimmiyar bincike kan lamarin.
Arewarmu.com A Yau Lahadi ta tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi DPS Kamal Datti Abubakar kan wannan lamarin inda ya shaida ma na cewa ya na ci gaba da tattara bayanai kan wannan lamarin ne, inda ya bukaci mu ba shi lokaci, domin shaida ma na komai. Ya zuwa aiko da rahoton bai kira mu ba.
Sunday, 17 September 2017
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
RELATED STORIES
Babbar magana: Gwamnatin tarayya za ta rushe wasu makarantun gaba da sakandire - Ministan IlimiBabbar magana: Gwamnatin tarayya za ta rushe wasu
Tofa! INEC za ta yi amfani da jakuna da kekuna wajen raba kayan zabe a Gombe Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC za ta dauki
ASUU zatai watsi da Gwamnati inji Shugaban Kungiyar Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya watau ASU
Sai Buhari ya sauka daga mulki zai iya gane munafukan sa - Sanata Shehu Sani Dan majalisar dattijai mai wakiltar mazabar j
An kashe mutane 66 a wasu unguwani a jihar Kaduna A kalla mutane 66 ne aka kashe a wasu ungu
MAHIMMANCIN ZABEN BUHARI A KARO NA BIYU GA YAN NAJERIYA.MAHIMMANCIN ZABEN BUHARI A KARO NA BIYU GA YAN NA
0 comments: