Sunday, 17 September 2017

Karshen Duniya Zai Fado A 23 Ga Watan Satumba 2017 – Masana

Wani kirista sannan kuma masani a bangaren harkar lissafi (Numerologist), David Meade, ya hango cewa karshen Duniya zai fado a ranar Asabar 23 ga watan Satumba, 2017.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na British Newspaper ta ruwaito cewa Meade ya ce, hakan zai faru ne ta sanadiyyar karo da wata Duniyar za ta yi da namu Duniyar (Earth).


Meade wanda ya bada ita wannan da’awar ya ce alamomin tashen Duniya da dama wadanda aka ce za su bayana kafin tashen Duniyar na ta faruwa a kusan ko ina da Duniya.

Meade ya ce ayar Luke 21: 25 zuwa 26 a littafin bibul ya nuna abubuwab da suka faru kamar su husufin hasken rana (Solar Eclipse) da kuma guguwar Harvey a kasar Amirka wato Hurricane Harvey duk wadannan abubuwa da suka faru suna cikin alamomin tashin Duniya.


Ayoyin sun karanto: “25: Za a nuna alamomin a ranar, wata da kuma taurari. A Duniya, kasashe za su kasance cikin damuwa sannan kuma za a tayar da teku. Mutane za su firgita saboda tsoro, suna jin tsoron abinda zai faru a Duniya, domin al’amuran sama za su girgiza.”


“26: Zuciyar mutane zai tsaya saboda tsoro, domin duba abubuwa da za su zo a Duniya: don al’amuran sama za su girgiza.”


“Da aka yi amfani da wadan su lambobi wato code, Littafin Bibul ta nuna ranar Asabar 23 ga watan Satumba 2017 ne ranar tashin Duniya”, Ya ce.


Meade ya gina ka’idarsa, a bisa ganin wani ruwan tabaru mai ban mamaki wacce ake kira da suna Duniyar X wato Planet X wanda fi sani da suna Nibiru. Yayi imanin Planet X za ta yi karo da Duniya a ranar 23 ga watan Satumba, wanda zai yi haifar da hadari kamar aman wuta daga cikin duwatsuna (Volcani Eruption), Ambaliyar ruwan tekuna (Tsunami) da kuma girgizan kasa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: