Korarriyar jarumar nan ta Kannywood, Rahama Sadau ta samu karramawa na musamman, inda aka zabe ta a matsayin deaya daga cikin wadanda zasu yi aikin gabatarwa a gagarumin bikin karramawa na Nollywood wato shirin nan na Best of Nollywood Awards (BON) na wannan shekaran. Dayan shi ne wani fitaccen dan wasan kudu mai suna Gbenro Ajibade.
Za’a gudanar da bikin ne a ranar Asabar, 16 ga Disamba, 2017 a garin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Gwamnatin Jihar Ogun din ce ta dauki nauyin shirya bikin a wannan shekarar.
Za’a gudanar da bikin ne a ranar Asabar, 16 ga Disamba, 2017 a garin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.
Gwamnatin Jihar Ogun din ce ta dauki nauyin shirya bikin a wannan shekarar.
0 comments: