Thursday, 12 October 2017

Kannywood: Har yanzu da sauran kuruciya ta - Rukayya Dawayya

Fitacciyar jarumar nan tsohuwar fuska a fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood watau Rukayya Dawayya ta fito tayi fatali da kiraye-kirayen da jama'a ke yi mata na ta yi aure inda tace ita fa har yanzu yarinya ce karama.

Shahararriyar jarumar da ta taka muyimmiyar rawa a fina-finai da dama tare kuma da bada gudummuwar ta musamman ma wajen habakar masana'antar ta ayyana cewa ita duka-duka yanzu shekarar ta 29 a duniya.


Arewarmu.com a cikin wani dan nazari da tayi game da zancen nata ta binciko cewa indai har hakan ta tabbata to lallai kenan jarumar tana da shekaru 13 kacal a duniya ne ta fito a cikin fim din Dawayya.

Shi dai fim din Dawayya kamar yadda binciken namu ya tabbatar, an shirya shi ne a shekara ta 2001 wanda yanzu kimanin shekaru 16 kenan.

A lissafi kenan idan aka cire shekaru 16 daga cikin 29 ya zama shekaru 13.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: