Saturday, 25 February 2017

Rikicin shugabanci Tsakanin Boko Haram: Shekau ya kashe kakakinsa

Rashin jituwa sakanin shugabanin kungiyar ‘yan ta’adda Boko Haram ya sanadiyar kisan kakakin shugaban, Abubakar Shekau.
Ainihin shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ya amince da kisan kakakin bangaren kungiyar kan wani makirci hambarar da shi, ya ce a cikin wata sautin rikodi wadda aka samu ta hanyar AFP.
A cikin sautin na minti 50 a wani taro da sauran ‘yan kungiyar, Shekau ya ce ya kashe "Tasiu" wanda aka sani da Abu Zinnira, wanda kuma ya fito da dama a wasu bidiyon saƙonnin kungiyar.

Ya ce: "Ya kamata ku ji ni da kyau, na kashe Tasiu" ya gaya wa taron da harshen Hausa wadda shi ne yaren da ake amfani a fadin arewa maso gabashin Najeriya.

Shekau ya bayyana ranar da aka gudanar da taron, 18 ga watan Disamba, 2017, ya ce ya kira taron domin tattauna a kan wadanda suke gunaguni a kan kisan Tasiu.

AFP ya samu kwafi na rikodi a farkon wannan watan. Kaset wadda aka raba sakanin ‘yan kungiyar .

Ku biyomu a
https://www.facebook.com/Arewarmu1
https://www.Twitter.com/Arewarmu1
https://www.Instagram.com/Arewarmu1

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: