Tuesday, 28 February 2017

Shirin Da Gwamnatin Buhari Takeyi Akan 'Yan Neja Delta - Osinbajo

Gwamnatin tarayya na wani shiri a Yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur
– Za a kashe fiye da Dala Biliyan 20 domin wannan aiki.
– Fiye da mutane 250,000 za su samu aiki idan har aka kammala aikin.
Gwamnatin tarayya na shirin gina wani wurin aiki a Yankin Neja-Delta da zai taimakawa Yankin ya kuma samar da ayyuka akalla 250,000. Mukaddashin shugaban Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana haka.

Wannan wuri da za a gina dai zai kai tsawon kilomita 60 inda za a rika ayyukan mai. Idan har an ci ma wannna buri za a rika samun sinadarin methanol da sauran sinadarai da ake samu daga danyen mai har ma da sinadarin hada takin zamani.
Farfesa Osinbajo yace duk wannan yana cikin muradun shugaba Buhari na tallafawa Yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur. Za dai ayi wannan aiki ne a Garin Ogidigben da ke Jihar Delta. Mutanen kasar Sin da Larabawa ne dai ake sa ran za su yi wannan aiki.

Yanzu haka dai Farfesa Osinbajo ke rike da Najeriya ya kuma yi ayyuka tafiyar shugaba Buhari na a-zo-a-gani. Kadan daga ciki su ne sauyi da aka gani a tsare-tsaren harkar kudin kasar daga CBN. Farfesa Osinbajo kuma ya shiga lungunan Neja-Delta domin kwantar da rikicin da ke Yankin.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: