Tuesday, 28 February 2017

Gwamnatin Kano Ta Maka Mawaki A Kotu Saboda Yayi Wakar Yabo Wa Kwankwaso

Gwamnatin jihar Kano ta maka wani matashin mawakin Hausa mai suna Sadiq Zazzabi a kotu ta 3 da ke jihar domin ya bada ba'asi kan wakar da yayi wa Kwankwaso

- Gwamnatin ta Kano ta ce tana tuhumar mawakin ne dai bisa zargin kin mika wakar tasa ga hukumar tantance harkokin fina-finai ta jihar kafin ya sake ta.
Shi dai Zazzabi ya saki wakar ne wadda ya yabi tsohon gwamnan Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwansao a kwanan baya.

A kwanakin baya ne dai Shugabannin jam’iyyar APC suka nada sabon kwamiti domin shirya wadansu ‘ya’yan jam’iyyar da ba sa ga maciji a tsakaninsu.

Jam’iyyar ta ce ta yi hakanne domin hada kan ‘ya’yan jamiyyyar a jihohin da ake da matsaloli tsakanin jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar.

Ana dai samun irin wadannan matsalolin akalla jihohi 12 da jam’iyyar ke fama da su.

Wasu daga cikin rikicin da jam’iyyar ke fama da su sun hada da: Rikicin gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai da Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani da kuma jihar Kano tsakanin gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wadanda suka fi muni a cikin su.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: