Wani barawo ya gamuda fushin kanikawa inda yaci na jaki bayan da jama’a suka dirar masa da fushin satar da yayi a unguwarsu a baya, bayan ya sake komawa unguwar da nufin sake cin banza
Wannan lamari ya faru ne a layin Ugo, cikin karamar hukumar Idemili na jihar Anambra yayin da wani barawo daya ji dadin satar waya ya koma unguwar da yayi satar a fari, don maimaita halin beran nasa.
Wata majiya mai tushe ta bayyana mana cewar barawon ya saci wata waya a garejin wasu kanikawa a satin data gabata, amma sai yayi rashin sa’a ya sake dawowa unguwar don kara satar wata wayar, nan ne fa dubunsa ta cika, yayin da wani mutum ya gane shi, kuma ya kwarmata ihu.
Yayin da wani shedan gani da ido Uchenna Muoghalu yake bayani, yace:
An kama barawon ne bayan ya saci wata waya satin data gabata, amma daya shiga hannu sai yayi nuni ga wasu mutane guda biyu daya ce sune abokan satan nasa, nan da suma aka far musu da duka, garin haka aka sumar da daya, dayan kuwa ya sha ruwan duwatsu.

0 comments: