Monday, 27 February 2017

Wannan Haka Yake: Naira Naci Gaba Da Kara Daraja(Karanta Cikakkun Bayanai)

Duk da cewa darajar Naira bai karu ba idan aka dan ganta da dala a yau Litinin, amma darajar tata ta karu idan aka dan ganta ta da kudin tarayyar turai na 'Euro' da kuma kudin kasar Ingila (Pound) inda yanzu ake saida su a matsayin N480 da kuma N565.
A ranar Litinin din da ta gabata dai ne CBN ya sanar da cewa ya fitar da wadansu sababbin manufofin musayar kudaden waje.


A karkashin sabon tsarin, Babban Bankin ya ce zai kara yawan kudaden wajen da ya ke bai wa bankunan kasar da nufin saukakawa 'yan Najeriya masu bukatar zuwa asibiti a wasu kasashen, da masu karatu a wasu kasashen da kuma 'yan kasuwa.

Farashin dala dai ya fadi sosai a karon farko a kasuwannin bayan fage na NAjeriya, kasa da mako guda bayan da babban bankin kasar CBN, ya bayyana matakin bunkasa samar da ita ga masu nema a bankuna.

Matsalar karancin dala a bankunan Najeriya wanda sakamakon rashin wadatar kudaden kasashen wajen a CBN, ya sa dalar ta yi ta tashin gwauron zabi, a kasuwannin bayan fage na kasar.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: