Sunday, 5 March 2017

Musha Dariya: Ka Ji Amfanin Abin Ko!!!

Wata mata ce ta auri miji siriri mara nauyi ita kuma irin matan nan ce mai kiba ga tsawo. Suna nan rannan a kwance tsakar gida da yaranta da maigidan, sai hadari ya taso kawai kafin ta ankara taji ruwa ya sauka ga fitila ta mutu sai tayi sauri ta dinga surar yaran tana kai su daki can tazo kan na karshen ta taba shi tace. Maigida!, Maigida!!, tashi ana ruwa. Sai taji daga daki muryar maigidan na cewa maman Fatima, ai ni ki ka fara dauka ki ka kai daki😂😂😂😂…..

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

1 comment: