Sanata Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya ya nuna rashin jin dadi game da kudurorin gwamnati masu gallazawa Jama'a a Najeriya.
-Shehu Sani ya damu ganin yadda kudurorin gwamnati a Najeriya ke rikidewa zuwa mulkin mulukiya.

Sanata Sani ya damu ganin yadda kudurorin gwamnati a Najeriya ke rikidewa zuwa mulkin mulukiya.
A wata ’yar gajeriyar sanarwa da ya yi a shafikansa na dandalin sadazumunta da muhawara r a yammacin Juma'a 3 ga watan Maris, Sani ya ce hana mutane taro da wasu kudurorin gwamnati babbar alama ce da ta ke nuna gwamnati na nema ta zama ta mulkin mallaka.
Sannan ya ce, bijirewa umarnin kotu da gwamnati ke yi da hana taruwar mutane kamar yadda doka ta bada dama, wasu alamu ne na mulkin mallaka.
Duk da cewa bai ambaci sunan shugaba Muhammadu Buhari ko wata jiha da ake ganin an aikata abubuwan da ya zayyana a jawabin nasa ba, ana zargin gwamnati mai ci yanzu da wasu daga cikin abubuwan da ya yi korafi a kai.
Kalaman na Sani na zuwa ne kimanin sa'o'i 24 bayan gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya sanya hannu a dokar da ta hana duk wani taron jama'a da ba ya kan doka a ko ina a fadin jihar.
An sanar da dokar ne ranar ranar Alhamis 2 ga watan Maris a Katsina a wata sanarwa da babban mai taimakawa gwamna kan yada labarai, Abdu Labaran ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce:
"Gwamna Masari ya bayyana cewa, duk wani taron mutane biyu ko fiye da haka a kowane bangare na jihar Katsina haramtacce ne.
"Ko da wane irin suna aka kira taron; ko mutanen na dauke da makamai ko kuma wani daga cikin su na dauke da makamai ko kuma duk wani abu mai hadari da ka iya kisa ko jin rauni to an hana wannan taro."

0 comments: