Gwamnoni sun ce ba za su bar aikin su ba domin zuwa ganin shugaba Buhari
– Gwamnonin suka ce babu dalilin yin haka domin kowa ta kan sa yake
– Abdulazeez Yari ya bayyana haka a jiya
Shugaban Gwamnonin Najeriya Abdulazeez Yari ya bayyana cewa Gwamnonin Najeriya ba su da wani shiri na zuwa duba shugaba Muhammadu Buhari da ke Landan. Yari yace babu wani dalilin yin hakan.
Shugaba Buhari dai yana Landan tun tsakiyar watan Junairu inda yace zai yi kwanaki 10 rak, sai ga shi dai ya buge har yanzu bai dawo ba. shugaban Gwamnonin Najeriya Abdulazeez Yari yace babu wani shiri da Gwamnoni suke yi na zuwa duba shugaban kasar.
Yari yace Gwamnoni ba za su iya barin aikin da ke gaban su duk su taru a Landan domin duba shugaba Buhari ba. Yari yace mafi yawan Gwamnonin sun yi waya da shugaban kasar har da shi don haka babu dalilin tafiya har inda yake domin yana samun sauk
Gwamnan yace ba abin mamaki bane don shugaba Buhari ya kwanta rashin lafiya inda aka duba shekarun sa da kuma ayyukan da ke gaban sa. Gwamnan yace sai dai ‘Yan Najeriya na ta kokarin yi wa shugaban na su addu’a.

0 comments: