Wednesday, 2 August 2017

Akwai Matsala: An rufe majalisar tarayya har tsawon sati 8 (Karanta Dalili)

Labarin da muka samu ba da dadewa ba yana nuni da cewa yan majalisar mu na tarayya da suka hada da majalisar dattijai da kuma majalisar wakillai sun rufe majalisar sun tafi hutun sati 8.

Mun samu labarin cewa shugaban majalisar ta tarayya watau Sanata Bukola Saraki ne bayyana hakan a zauren majalisa a jiya kafin rufe zaman na ta.

Arewarmu.com ta samu labarin cewa dai kafin a rufe majalisar yan majalisun sun yi ta yin sauri suna kammala sauran ayyukan da suka rage masu domin samun damar tafiya hutun.

Binciken mu kuma ya tabbatar mana da cewa wannan hutun dai na majalisar baya rasa nasaba da lokacin zuwa hajji da yayi wanda kuma musulmai da dama a cikin yan majalisun kan halarta a duk shekara.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: