Tuesday, 1 August 2017

Yadda aka daure yaro har kwana 3 a bisa zargin kasancewa Aljani

Austin Segun uba ne ga yara uku a al'umman Eruemukohwarien a karamar hukumar Ughelli ta gabas a jihar Delta wanda ya daure hannayen da kafafun dansa ya hada igiyar da karfen windo a gidansa har tsawon kwana uku bayan wani Pasto ya shaida masa cewa yaron Aljani ne.
Bayanai sun nuna cewa 'yan banga ne suka ceci yaron a yayin da suka ji yana nufashi da kyar da misalin karfe 2:00 na dare kuma suka shaida wa DPO na sashe na "A" wanda shi kuma ya kama mahaifin yaron.


Rahotanni sun nuna cewa yaron ya shaida wa yansanda cewa ya sha fama da irin wannan gallazawa saboda mahaifiyarsa ta rasu kuma haka yake shan azaba a hannun kishiyar uwarsa.

'Yansanda sun kai yaron babban Asibiti na Ughelli inda aka duba lafiyarsa.

A bisa wannan dalili ne dattijan garin Ughelli suka yi zaman gaggawa inda suka kori Austin da matarsa daga garin Ughelli.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: