Tuesday, 1 August 2017

Kannywood: Jaruma Fati Muhammad ta bayyana babbar nadamar ta a rayuwa

Fitacciyar tsohuwar jarumar nan Fati Muhammad wadda ta fito a cikin tsohon fim din nan na Sangaya a matsayin Zubaina ba bayyana auren jarumi Sani Musa Mai Iska a matsayin babbar nadamar ta a rayuwa.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da jaridar Blue Print inda ta bayyana cewa ta amince da cewa kowa na da jarabawar da Allah ya ke yi masa sannan kuma tace ita dai jarabawar ta ta fannin aure take.
Arewarmu.com ta samu cewa a cikin firar da tayi da jaridar, jarumar ta kara nanata maganarta da tayi a baya inda tace ba fa zata kara auren dan fim ba koma waye.

Daga karshe kuma jarumar ta bayyana jarumi Ali Nuhu a matsayin wanda take darattawa fiye da kowa a masana'antar fim.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: