Tuesday, 1 August 2017

Wasikar wani Dan Najeriya ga Shugaban kasa Buhari

- Wani Dan Najeriya ya aikawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika

- Wannan mutumi yace yanzu an fara kira Kai Baba maimakon Sai Baba

- Yace Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari yayi murabus

A farkon makon nan Wani Dan Najeriya ya aikawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasika wanda yanzu yana can yana jinya.
Wannan mutumi yace yanzu Jama'a sun fara kiran Kai Baba maimakon Sai Baba da su ka saba fada. Wannan mutumi yace yana rokon Shugaban kasar Buhari yayi murabus don kuwa hakan ne abin da ya dace.

Wannan mutumi yace ba ya cikin masu yi wa Shugaban kasar adduar ya mutu. Haka kuma yace bai damu don Shugaban kasa Buhari ya samu lafiya ba. Yake cewa kurum abin da yake so ya ga Shugaban kasar ya ajiye mulki ya huta.

Yace Najeriya fa ba akulkin Shugaban kasa Buhari bace don yanzu haka tattalin arziki ya shiga matsala inda kuma Alkalai sun zama abin da su ka zama ita kuma Majalisa an kassara ta. Mark Anthony yace tun da girma Buhari ya ajiye mulki.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: