Saturday, 19 August 2017

Kannywood: Babban buri na in kayatar da mutane - Nafisa Abdullahi

Shahararriyar jarumar nan ta wasan Hausa mai suna Nafisa Abdullahi wadda aka fi sani da Nafisa Sai wata rana ta bayyana cewa ita fa babban burin ta shine ta kayatar da mutanen da suke kallon fina-finan ta.

Shahararriyar jarumar ta yi wannan kalamin ne lokacin da wata majiyar mu ke yin fira da ita ake kuma tambayar ta al'amura da dama a rayuwar ta musamman ma game da harkar fina-finai.

Arewarmu.com ta samu cewa da aka tambaye ta ko meye dalilin da kwana biyu ba'a cika ganin ta a cikin sabbin fina-finai ba sai ta kada baki tace ta dan samar wa kanta wani dan hutu ne tana nazari yadda zata fitar da wani mashahurin fim din ta da zai kayatar.

Da aka tambaye ta ko meye sunan fim din sai ta ce sunan fim din 'Karma' kuma ma yanzu haka an ci karfin shirin don ma kuwa an kusa kammala shi saura kadan.

Duk da cewa jarumar taki ta bayyana abun da fim din ya kunsa, amma dai tayi wa dumbin masoyan ta albishir da cewa tabbas fim din zai kayatar sosai matuka.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: