Saturday, 19 August 2017

Albashin na na miliyan 8 kwana 7 kawai yake yi mani - Gudaji Kazaure

Dan majalisar nan na tarayya mai wakiltar mazabar kananan hukumomin Kazaure, Roni, Yankwashi da kuma Gwuiwa ya fito fili ya fadawa duniya cewa shi fa albashin sa da mutane ke ta fada kwana 7 yake yi masa shikenan ya rabar da shi ga al'umma.

Dan majalisar dai yayi wannan ikirarin ne lokacin da yake zantawa da jama'ar mazabar sa da suka je masa ziyara inda ya bayyana cewa shi kudin sa ba na ajiye wa bane da ya samu yake bayar wa.

Arewarmu.com ta samu dai cewa dan majalisar kuma ya kara da cewa sauran sati 3 ko kuma kwanaki 21 zuwa 23 na watan duk da rufa-rufa yake ida su don kuwa dukkan abun da ya mallaka ya riga da ya rabarwa jama'ar sa.

Mai karatu dai tuna cewa a kwanan baya ma dai dan majalisar a cikin wata fira da yayi da gidan rediyon Dala a Kano ya roki mabiya addinin shi'a da su ji tsoron Allah su bar yi wa shugaba Buhari munanan addu'oi.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: