Daga Muhammad A. Abubakar
Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa dole ne a kamo wadanda ke da hannu a kai hari kan al’umman hausawan da ke zaune a Kudu; kuma idan an kamo dole ne a hukunta su.
Sarkin ya bayyana haka ne a hudubarsa ta ranar Juma’a 15 ga watan Satumbar 2017, a masallacin gidan Sarki da ke Birnin Kano.
Sarki Sanusi II ya janyo hankalin jami’an tsaro da shugabanni da su tuna cewa nauyi ne day a rataya a wuyansu na su kula da rayuka da dukiyoyin al’umman Nijeriya, wannan kuma ya hada har da rayukan Musulmin da ake kashewa a kudanci kasar.
Sannan Sarkin ya gargadi al’umma da su guji yin aiki da jita-jita, keta, da kuma cutar da mutumin da bai aikata laifin komi ba, saboda Allah madaukakin sarkiyayi hani da hakan.
Ya ce; “Muna samun rahotannin irin abubuwan da ake yiwa ‘yan uwanmu a Kudancin kasar nan. Mu na tunatar da kawunanmu cewa musulunci addini ne da aka gina shi akan tsarin tsantsani, da aminci.”
Ya kara da cewa Kiristoci kuma ‘yan Kudun da ke zaune a garin Kano, suna karkashin amanar al’umma ne, kuma ya haramta a kaddamar da farmaki akansu. “Saboda Allah ma cewa yayi kar ku yi mu’amala da wadanda suka kaddamar da hari akanku, suka kashe ku, ko suka bayar da gudummawa wurin kashe ku, ko kuma suka tursasa muku yin hijira daga gidajenku.”

0 comments: