Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Gareth Bale yace baya jin haushin ihun da magoya bayan kungiyar suke masa inda ya bayyana cewa kwallon kafa da cewa dama ta gaji haka.
Dan wasan dai yana shan suka daga wajen magoya baya da yan jaridu a kwana-kwanan nan musamman a wasanni biyun da kungiyar ta buga a gida kuma ta buga canjaras da kungiyoyin Balencia da Lebente.
Bale, dan shekara 28 ya bayyana cewa duk da irin ihun da magoya bayan suke masa baya jin dadi, amma kuma bazai nuna rashin jin dadinsa saboda magoya baya sune kashin bayan kungiya.
Sai dai dan wasan yazura kwallo a wasan da kungiyar ta lallasa kungiyar Real Sociedad a wasan laliga sati na hudu.
Dan wasan dai a kwanakin baya ya bayyana yadda yakusa komawa Manchester united kafin daga baya ya canja shawara kuma ya taimakawa kungiyar ta real Madrid ta lashe kofin laliga da gasar zakarun turai.

0 comments: