Tuesday, 29 August 2017

Ina nan a kan baka ta: Nan gaba kadan zan saye Arsenal Inji Dangote

Alhaji Aliko Dangote yayi hira da Jaridar Bloomberg ta Turai inda ya kara jaddada matsayar sa yace nan gaba kadan zan saye Kungiyar Arsenal.
Dangote dai ya bayyana cewa da zarar ya kammala aikin da yake yi na matartar mai a Kasar zai dunfari sayen Kungiyar Arsenal kuma yace yana ganin idan yayi tayin kwarai za a saida masa kulob din da ya dade yana goyon baya komai runtsi.

Aliko Dangote ya kashe kusan Dala Biliyan 18 wajen harkar kasuwanci a Yankin na Afrika wajen harkar abinci da siminti yace bai dace ace a rika shigo da wani abinci Afrika ba don kuwa akwai duk abin da ake bukata na noma daga yanayin kasa har ruwan sama.

Alhaji Dangote yana gina matatar man da babu irin sa a Duniya yanzu haka wanda shi ne karo na farko da ya tsunduma harkar fetur.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: