Sanata Dino Melaye dake wakiltar al’ummar Kogi ta yamma yayi bajakolin motocinsa na alfarma guda dai dai har goma sha takwas a shafins na Instagram.
Arewarmu.com ta ruwaito Sanatan da baya rabuwa da shiga bakin jama’a yayi ma hotunan motocin taken ‘Kayan wasa na, abin so na, duk zaku fada, ku fada.’
Wasu daga cikin motocin da Dino Melaye ya daura hotunansu sun hada da G-Wagon, Rolls Royce, Bentley, Ferrari da sauran manyan motocin alfarma da kudadensu sai dai dinga lissafin daruruwan miliyoyi.
Sai dai hakan ya takulo ra’ayoyi daban daban daga yan Najeriya, inda wasu suka tofa albarkacin bakinsu kamar haka; wani cewa yayi, "kana siyan abinda baka da bukatarsu, amma ka sani alfahari ba burgewa bane."
Wani ma’abocin Instagram mai suna Benjisazi cewa yayi “Ba zan taba kiranka barawo ba, don kuwa nima so nake nayi kudi kamar ka, kuma ina so in yi suna a siyasan Najeriya, don haka a cigaba da gashi.”
Source: Naij.com Hausa

0 comments: