Saturday, 7 October 2017

Kannywood: Shekaru 3 muna soyayya da Nafisa Abdullahi kafin mu watse - Adam A. Zango

Fitaccen jarumin nan na wasannin fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood kuma jigo a harkar Adam A. Zango ya fito ya shaidawa duniya cewa ya shafe shekaru akalla uku kafin su bata kowa ya kama gaban sa.

Adam A. Zango dai wanda ake yi wa lakabi da yariman mawaka watau Prince da kuma yanzu haka yake da mata biyu na aure ya bayyana cewa sun tafka mahaukaciyar soyayya inda kuma har ta kai ga sun kusa yin aure amma sai kaddara ta riga fata.


Arewarmu.com dai ta samu cewa shahararren dan fim din kuma mawaki ya dai ki fitowa fili ya fadawa duniya meye musabbabin rabuwar ta su amma dai ya bayyana cewa kawai dai kaddara ce ta raba su kuma daman can Allah bai nufi zata zama matar sa ba.

Idan mai karatu dai zai iya tunawa mun kawo maku wani rahoto a kwanan baya inda Nafisa Abdullahi din ta bayyana cewa ba zata auri dan fim ba kuma ta kusa yin auren.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: